Rikici ya ɓarke tsakanin jami’in Soja da ministan Abuja Wike, kan wani fili da ake taƙaddama akansa
Ministan Abuja Nyeson Wike, sun yi cacar baki da sojoji kan rikicin filaye da ake takaddama a kai a birnin tarayya Abuja, a Gundumar Gaduwa da ke Abuja.
Lamarin ya faru ne lokacin da aka ruwaito sojoji sun hana Wike da tawagarsa shiga filin, wanda hakan ya haifar da musayar kalamai tsakanin tawagar ministan da jami’an sojoji. “Wannan ba shi da ƙwarewa. Ba za ka iya yi wa minista barazana kamar wannan ba,” inji mai tsaron Wike.
Cikin fushi a rikicin, Wike ya yi tambaya game da ƙarfin ikon sojojin da kuma halascin mallakar filin, yana zarginsu da yin aiki ba bisa doka ba. “Ba ka da takardu,” in ji Wike.
KU KUMA KARANTA: Wike da Jami’in Soja: Shugaban ƙasa ne kaɗai ke da ikon soke umarnin Soja – Barista Abba Hikima
Wike yana zargin cewa ba a bi ƙa’idoji masu kyau ba a mallar filin. “Ba za mu iya ci gaba da yin aiki ba tare da hukunci ba. Ba za ka iya zama sama da gwamnati ko amfani da bindigogi don tsoratar da kowa ba. Ni ba ɗaya daga cikin waɗanda za ka iya tsoratarwa ba ne.” Wike yake gayawa matashin Sojan da ya hana shi shiga filin.
Ministan ya ƙara yin Allah wadai da abin, inda ya bayyana hakan a matsayin rashin girmama ikon farar hula da sojoji suka yi, yana mai dagewa cewa babu irin wannan dokokin mallakar fili a cikin bayanan Hukumar FCT (FCTA).

“Abin takaici ne ƙwarai da gaske,” in ji Wike, yana mai nuni da kalaman da ake zargin wani tsohon babban Hafsan Sojoji ya yi game da ƙasar. “Ban fahimci yadda wani wanda ya kai wannan matsayi ba zai iya zuwa ofishina don warware matsalar ba, amma maimakon haka ya yi amfani da ƙarfin soja don tsoratar da ‘yan Najeriya. Ba zan yarda da cin zarafi ba.” Duk da ƙin amincewar ministan, an ruwaito cewa sojojin sun ƙi barin wurin, suna mai da’awar cewa suna aiki ne bisa umarnin tsohon babban Hafsan Sojojin Ruwa, Vice Admiral Zubairu Gambo.
Rikicin ya nuna tashin hankali da ake ci gaba da yi game da kula da filaye da kuma shigar sojoji cikin taƙaddamar kadarori a cikin babban birnin tarayya Abuja.









