Wike da Jami’in Soja: Shugaban ƙasa ne kaɗai ke da ikon soke umarnin Soja – Barista Abba Hikima
Fitaccen lauya kuma mai sharhi kan harkokin doka da tsaro, Barista Abba Hikima, ya bayyana cewa Shugaban ƙasa ne kaɗai, a cikin farar hula da ke da ikon doka na soke umarnin jami’in soja, wanda ya hana Ministan Abuja, Nyesom Wike, shiga wani fili da ake taƙaddama akai a babban birnin tarayya Abuja.
Barista Hikima, wanda ya bayyana haka a shafinsa na Facebook, ya ce ko Ministan tsaro ba shi da ikon soke umarnin aiki da aka bai wa jami’in soja, sai dai idan an bi matakan hukuma na cikin tsarin rundunar soji.
KU KUMA KARANTA: Wike ya ci tarar Ganduje, Idiagbon da Oyinlola kan amfani da filaye ba bisa ƙa’ida ba
A cewar sa, Wike bai da wani matsayin umarni a kan jami’an da ke wurin, don haka da ya tuntuɓi manyan hukumomin soja ta hanyar da ta dace, da bai gamu da abin kunya ba.
Ya ƙara da cewa, jami’in sojan da ya hana Wike shiga yana bin umarnin manyansa ne, kuma idan da ya bari ministan ya shiga filin da ake magana a kai, da ya aikata laifin ƙin bin umarnin doka.
Barista Hikima ya kammala da cewa lamarin ya zama darasi ga shugabanni na farar hula da su riƙa bin tsarin doka da sadarwa ta hukuma wajen hulɗa da jami’an tsaro, musamman ma na rundunonin soja.









