Majalisar Yobe ta zartar da ƙudirin gyara tsarin gudanarwa na manyan makarantu mallakin jihar
Majalisar Dokokin Jihar Yobe ta zartar da ƙudirin doka da ke neman gyara tsarin majalisun gudanarwa na manyan makarantu biyar a jihar.
A zaman majalisar na ranar Alhamis, Kakakin Majalisar, Hon. Chiroma Buba Mashio, ya karanta ƙudurorin Majalisar, bayan haka aka ba da damar ƙudirin ya ci gaba zuwa karatu na uku sannan aka zartar da shi.
Sabon ƙudirin da aka zartar ya shafi waɗannan makarantu:
– Mai Idriss Alooma Polytechnic, Geidam
–College of Administrative Management and Technology Potiskum
–College Agricultural, Science and Technology Gujba
– Umar Suleiman College of Education, Gashua
– College of Education and Legal Studies, Nguru
A cewar Majalisar, kwaskwarimar tana da nufin ƙarfafa tsarin shugabanci na cibiyoyin da kuma inganta ƙarfinsu na biyan buƙatun amincewa.
KU KUMA KARANTA: Gwamnan Yobe ya ƙaddamar da tallafin Naira biliyan 2.93 ga waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa
Ɗaya daga cikin muhimman sakamakon ƙudirin dokar shi ne cewa ya ba Kwalejin Ilimi ta Umar Suleiman, Gashua, da Kwalejin Ilimi da Nazarin Shari’a, Nguru, damar fara shirye-shiryen digiri a fannin ilimi da sauran fannoni masu alaƙa. Za a gudanar da waɗannan shirye-shiryen ta hanyar tsarin yanayi biyu, bisa ga jagororin Hukumar Jami’o’i ta Ƙasa (NUC) da Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya.
‘Yan majalisar sun ce gyaran zai kuma inganta matsayin ilimi na cibiyoyin tare da samar da ƙarin damammaki ga ɗalibai a jihar don neman ilimi mai zurfi a cikin shirye-shiryen da aka amince da su.









