‘Yanbindiga sun sace mataimakin shugaban majalisar dokokin jihar Kebbi
Ana zargin ‘yan bindiga sun yi garkuwa da Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kebbi, Hon. Samaila Bagudo.
Daily Trust ta rawaito cewa rundunar ’Yansanda ta tabbatar da cewa an sace dan majalisar ne a garinsu da ke Karamar Hukumar Bagudo, bayan ya idar da sallar Isha’i a daren Juma’a, 31 ga Oktoba, 2025, da misalin karfe 8:20 na dare.
KU KUMA KARANTA: Sulhu da ‘yan bindiga ba tare da karɓe makamansu ba, tamkar miƙa wuya ne – Gwamnan Zamfara
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, CSP Nafiu Abubakar, ya fitar, an bayyana cewa an tura hadakar jami’an tsaro da suka hada da rundunar ’yan sanda da sojoji da jami’an sa-kai domin ceto dan majalisar.
Sanarwar ta ce, “Jami’an tsaron hadin guiwa suna ci gaba da bincike a hanyoyin da ake zargin ’yan bindigar suke bi da dazukan da ke kewaye, domin ceto dan majalisar ba tare da wani rauni ba, tare da cafke wadanda suka aikata wannan aika-aika.”









