Majalisar dokokin Najeriya ta amince shugaba Tinubu ya sake ciyo bashi
Majalisar dokokin Najeriya ta amince da bukatar shugaban ƙasa, Bola Tinubu, na karɓo bashin dala biliyan 2.347 daga kasuwannin hada-haɗar kuɗi ta duniya domin cike giɓin kasafin kuɗin 2025 da kuma sake biyan takardun lamuni na Eurobonds da ke ƙarewa.
Tinubu ya bayyana cewa bashin zai kasance bisa tanade-tanaden dokar kula da bashi ta 2003, wadda ke buƙatar amincewar majalisa kafin ɗaukar sabon bashi ko sake biyan tsoffin bashi.
KU KUMA KARANTA: Idan ba a yi wasa ba Tinubu zai fara ciyo bashi a Opay da Moniepoint da Palmpay – Dino Melaye
Shugaban ƙasa ya ce za a samo kuɗin ne ta hanyar kayan aikin kuɗi kamar Eurobonds da haɗin bashi daga bankuna, ko wasu hanyoyin wucin gadi dangane da yanayin kasuwa.









