Cin Zarafin ‘Yan Jarida: Gwamnatin Kano ta ƙaryata wani rahoton da Cibiyar Bincike ta Wole Soyinka ta fitar
Daga Jameel Lawan Yakasai
Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Kano, Kwamrade Ibrahim Abdullahi Waiya, ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai da aka gudanar a yammacin Laraba 29 ga Oktoba 2025.
Kwamishinan ya ce rahoton ba shi da tushe kuma bai bayyana hakikanin yanayin hulɗar gwamnati da kafafen yaɗa labarai a jihar ba, inda ya jaddada cewa gwamnatin Alh. Abba Kabir Yusuf tana mutunta ’yancin faɗar albarkacin baki da ayyukan jarida.
KU KUMA KARANTA: Dalilan da ya sa labaran ƙarya ya fi yaɗuwa – Dakta Hassan Gimba, a hirarsa da RFI Hausa
Ya ƙara da cewa gwamnatin Kano tana da kyakkyawar alaƙa da ƙungiyoyin ƴan jaridu da kafafen yaɗa labarai, tare da ci gaba da samar da yanayi mai kyau don bunƙasa aikin jarida cikin ƴanci da gaskiya.









