‘Yan Fashi sun addabi anguwar Graceland da ke Zariya

0
122
'Yan Fashi sun addabi anguwar Graceland da ke Zariya

‘Yan Fashi sun addabi anguwar Graceland da ke Zariya

Daga Idris Umar, Zariya

Mazauna unguwar Graceland da ke cikin ƙaramar hukumar Sabon Gari ta Jihar Kaduna sun roƙi gwamnatin jihar Kaduna da ta ƙaramar hukumar Sabon Gari da su samar da ofishin ‘yan sanda a yankin, domin kare su daga hare-haren ‘yan daba da suka zama ruwan dare.

Da yake magana da manema labarai a Zariya, Malam Muhammad Abdullahi, wanda shi ne Mai Anguwan Yusi na Graceland, ya bayyana cewa duk da ƙoƙarin ‘yan sanda na yin sintiri a yankin, amma kusan kullum ‘yan daba na kai hari da fashi a gidajen jama’a.

Ya yaba wa jami’an tsaro bisa gaggawar amsawa idan aka sanar da su, yana mai fatan wannan kyakkyawar alaƙa za ta ci gaba da kasancewa.

KU KUMA KARANTA: An tsinci gawar yarinya Hanifa da ruwan sama ya tafi da ita a Zariya

A nasa bangaren, ɗaya daga cikin waɗanda abin ya shafa, Dr. Oche Friday, ya ce a ranar da ‘yan daba suka kai masa hari, sun ji masa rauni da makaman da suka yi amfani da su, sannan suka kwashe kwamfutarsa da wasu kayan ƙima.

Dr. Oche ya ƙara da cewa yawancin gidaje a unguwar sun sha irin waɗannan hare-hare daga ‘yan fashi.

Haka kuma wata mazauniyar yankin, Malama Ladi, ta roƙi ƙarin jami’an sa-kai (vigilante) domin taimaka wa wajen magance miyagun mutane da ke addabar al’ummar Graceland.

Ta ce duk da ƙoƙarin al’umma wajen kare rayuka kansu, suna buƙatar taimakon gwamnati domin samun cikakken tsaro. Malama Ladi ta yi addu’a cewa a tabbatar da adalci ga duk waɗanda aka kama bisa laifin da suka aikata wa mutane.

A yayin da yake gabatar da waɗanda aka kama, Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sanda ta Jihar Kaduna (PPRO), DSP Mansur Hassan, ya bayyana cewa, a ranar 15 ga Oktoba, 2025, ‘yan sanda na sashen Dan Magaji Division a Zariya sun samu bayanan sirri game da wasu mutane masu zargi a yankin Gwargwaje.

Da jami’an suka isa wurin, wasu mutum biyu sun yi ƙoƙarin gudu sannan suka bude wa ‘yan sanda wuta. Sai jami’an suka mayar da martani, suka rinjaye su da “ƙarfin makami.”

An kama ɗaya daga cikin su, Sadiq Idris (mai shekaru 21) daga Kumbotso, Kano State, tare da bindigar English pistol, harsasai guda biyar na 9mm, da kuma bindigar pump-action.

Bincike ya kai ga kama wani mutum mai suna Usman Aminu (mai shekaru 21) daga Panshekara, Kano, inda aka samu harsasai guda tara na 9mm a wurinsa.

Binciken da aka ci gaba da yi ya kai ga kama Abdulaziz Usman (25), Jibren Yahaya, Hajara Abdulkarim (20) da Fatima Alhassan (18) tare da wasu makamai da hujjojin da ke da alaƙa da laifukan.

Ya zuwa hawa wannan rahoton dai jama’ar wannan anguwa basa bari saboda barazanar da yan Sanar ki yin masu.

Sun kuma roki bangarorin yan siyasa da su tallafa masu da Akwatin Sola don haska titunan yankin .

Bincike ya nuna cewa ɓata garin na amfani da tsofaffin ginin da tsohon gwamnan jihar Kaduna ya rushe mallakar kwalejin koyan tukin jirgin sama a Zariya ( Aviation Zaria).

Bisa haka ne jama’ar yankin suke kira ga hukumomin tsaro da akwai masu dauki

Mutanen anguwar sun ce babban abin daya fi bata masu rai shine yadda yan’Daban kewa yaransu Fyaɗe a duk lokacin da suka kawo farmakin.

Yanzu haka jama’ar anguwar sun zura idanu suga wani taimako za ayi masu akan wanda ake masu.

Leave a Reply