Hisbah ta soke auren Idriss Mai Wushirya da Basira ‘Yar Guda

0
110
Hisbah ta soke auren Idriss Mai Wushirya da Basira 'Yar Guda
Mai Wushirya tare da 'Yar Guda

Hisbah ta soke auren Idriss Mai Wushirya da Basira ‘Yar Guda

Daga Jameel Lawan Yakasai

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta sanar da fasa gudanar da auren da aka shirya tsakanin fitattun masu amfani da Manhajar TikTok, Idris Mai Wushirya da Basira Yar Guda, bayan bincike ya gano cewa babu soyayya ta gaskiya kamar yadda suka bayyana a kotu.

Mataimakin Kwamandan Hisbah, Sheikh Mujahideen Aminuddeen, ya bayyana cewa binciken hukumar ya tabbatar da cewa mutanen biyu sun ƙirƙiri labarin soyayya ne kawai domin guje wa hukunci daga kotu, bayan sun fuskanci tuhuma daga Hukumar Censorship Board kan bidiyoyin da aka bayyana da suna “marasa dacewa.”

A baya kotu ta ba da umarni ga Hisbah da ta shirya aurensu cikin kwanaki 60 ko kuma a dawo da shari’ar kotu idan hakan bai yiwu ba.

KU KUMA KARANTA: Kotu ta umarci Hisbah ta ɗaura wa Ashiru Mai Wushirya aure da ‘Yar Guda nan da kwanaki 60

Sai dai Sheikh Mujahideen ya ce Hisbah ta dakatar da shirin auren saboda rashin amincewa daga ɓangarorin biyu da kuma gujewa auren da ba ya bisa yardar juna.

A cewar sa, “Mun gano cewa soyayyar ba ta gaskiya bace, kawai wasa da nishaɗi ne domin samar da abun kallo a TikTok, ba soyayya ta aure ba.”

Hukumar ta sanar da cewa za ta mika lamarin zuwa kotu domin ɗaukar matakin da ya dace.

Leave a Reply