An yi sulhu tsakanin Gwamna Abba Kabir Yusuf da Sheikh Daurawa

An yi sulhu tsakanin gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf da Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, shugaban hukumar Hisbah ta jihar wanda ya sauka daga muƙaminsa a makon jiya.

Mutanen biyu sun yi sulhu ne ranar Litinin ƙarƙashin jagorancin “Inuwar Haɗin Kan Malamai da Ƙungiyoyi” kamar yadda Sheikh Daurawa ya bayyana.

Ya ce malaman da suka shiga tsakani har aka yi sulhun sun haɗa da “Farfesa Barodo, Sheikh Abdulwahab, Farfesa Salisu Shehu, Farfesa Babangida da Farfesa Sa’idu Dukawa.”

Sauran su ne “Dr Mu’azzam Khalid BUK, Injiniya Bashir Hanan, Shaikh Shehu Mai Hula waɗanda suka wakilci sauran malamai.”

KU KUMA KARANTA: Jama’a na nuna fargaba kan makomar Hisbah bayan murabus ɗin Sheikh Daurawa

Malamin ya yi godiya a gare su, sannan ya ce hukumar Hisbah ta jihar Kano za ta ci gaba da “aiki daram ba sani ba sabo, tare da kiyaye doka.”

A ranar Juma’ar da ta gabata ne Sheikh Daurawa ya sanar da ajiye muƙamin nasa kwana guda bayan gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya caccaki hukumar ta Hisbah bisa salon ayyukanta waɗanda ya ce suna keta doka.

Sheikh Daurawa ya ce “gwiwoyina sun yi sanyi” bayan da ya saurari kalaman gwamnan kan sukar da ya yi wa hukumar Hisbah.

“Ina bai wa mai girma gwamna (Abba Kabir Yusuf) haƙuri bisa fushi da ya yi da maganganu da ya faɗa, kuma ina roƙon ya yi min afuwa. Na sauka daga kan wannan muƙami da ya ba ni na Hisbah. Kuma ina yi masa addu’a, ina yi masa fatan alheri,” in ji Malamin.

Tun da farko a ranar Alhamis, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce hukumar Hisbah ta jihar Kano tana aikata “kuskure babba” game da yadda take gudanar da wasu ayyukanta a yunƙurin yaƙi da masu aikata ɓarna.

Gwamna Abba Gida-Gida, kamar yadda aka fi saninsa, ya ce akwai kura-kurai da dama a salon da Hisbah take bi wurin kama masu aikata ɓarna musamman mata da matasa.

”An je inda wasu matasa ke ɓarna – maza da mata – amma yadda aka dinga ɗebo su ana duka da gora, suna gudu ana bin su da gora ana taɗe ƙafafunsu, ana ɗebo su kamar awaki a jefa su cikin mota (Hilux), wannan muna gani kuskure ne babba,” a cewar gwamnan na jihar Kano.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *