An yi sallah da addu’o’i kan halin tsananin rayuwa a Najeriya

1
353

Daga Ibraheem El-Tafseer

A jihar Kano an gabatar da Salloli tare da ruwan addu’o’i, kan halin matsin rayuwa da al’umma suke ciki a Najeriya. A yau Lahadi da safe ne, al-ummar ƙaramar hukumar Ungogo da ke jihar Kano, suka sake fita masallacin idi suka gabatar da Salloli tare da yin ruwan addu’o’i, domin Allah ya kawo mana ƙarshen musifa ta tsadar rayuwa, tsadar kayan masarufin da ake ciki wanda ba a taɓa yin irin sa ba a Najeriya.

Limamin da ya jagoranci addu’ar, ya yiwa Mutane nasihohi masu ratsa zuciya kan mutane su koma ga Allah, a daina saɓo, a taimaki mutanen da suke cikin mayuwancin hali. Limamin yace, yauce rana ta biyu gobe Litinin ma za su sake fita su ci gaba da gabatar da addu’o’in.

Mu ma muna Addu’ar Allah ya amsa addu’o’in da suka gabatar. Ya kamata sauran gagaruwa ma, su fara gabatar da irin waɗannan addu’o’in, domin wahalar da ake sha ya wuce duk yadda ake tunani.

1 COMMENT

Leave a Reply