An yi jana’izar mutanen da suka mutu a hatsarin kwale-kwale a jihar Neja
An gudanar da jana’izar mutane 31 cikin waɗanda suka mutu sakamakon hatsarin jirgin kwale kwale a jihar Nejan Najeriya.
Tun a cikin daren Talatar da ta gabata ne jirgin ruwan kwale kwalen ya kife da mutum sama da 300 da suka fito daga garin sabuwar Gwajibo ta jihar Kwara.
Mutanen na kan hanyarsu ta zuwa wani taron Maulidi ne a garin tsohuwar Gwajibo da ke yankin karamar hukumar Mokwa ta jihar Nejar.
Shugaban hukumar ba da Agajin Gaggawa ta jihar Neja Abdullahi Baba Arah y ace an samu an yi jana’izar mutum 31 da aka tsamo gawarwarkinsu a ranar Alhamis din nan bayan da aka samu mutane 150 da ransu.
KU KUMA KARANTA:Mutane 29 sun mutu a hatsarin jirgin kwale-kwale a Kongo
A lokacin hada wannan rahoto, gwanayen ninkaya na ci gaba da aikin lalubo mutum sama da 100.
Shugaban Hukumar HYPADEC Mai kula da Garuruwan da ke gabar ruwa masu tashohin samar da Lantarki a Najeriya Alhaji Abubakar Sadik, ya ce sun ba da cigiyar gawarwaki a sauran garuruwan da ke gabar wannan Kogi na Neja.
Masu sharhi akan al’amura na cike da fatar ganin hukumomin Najeriya sun Dauki mataki mai karfi da zai magance wannan matsala ta yawaitar samun hadurran jiragen ruwa a kasar wadanda ke haddasa asarar rayukkan jama’a.