An yi jana’izar Ɗanmajen Arewan Zazzau
Daga Idris Umar, Zariya
A ranar yau aka gabatar da Jana’izar Marigayi Injiniya Hayyatu Mustapha Danmajen Arewan Zazzau wanda Allah Yaima rasuwa da yammacin jiya a Babban Birnin Tarayya Abuja bayan fama da jinya.
Fittacen Malamin Addinin Musulunci na Zariya Malam Kasimu Aminu ya jagoranci Sallan Jana’izar Marigayi Danmajen Arewan Zazzau wanda Mai Martaba Sarkin Lere Alhaji Suleiman Umar da ‘Yan Majalisansa Masarautan Zazzau da Hakimai da dimbin Al’umma suka sami halarta. An kuma Binne Gawarsa a Makabartan Magajin Garin Zazzau wanda ke Anguwan Kwarbai cikin Birnin Zariya.
KU KUMA KARANTA:Mataimakiyar Sakatare-Janar ta MƊD ta kammala ziyarar aiki ta kwanaki 2 a Najeriya (Hotuna)
Marigayi Danmajen Arewan Zazzau mai shekaru Sittin da Uku da Haihuwa, tsohon Ma’aikacin Kamfanin matatan Mai Na Kasa ne watau (NNPC). Ya kuma bar Mahaifiyansa da Mata da ‘Ya’ya gami da ‘Yan Uwa da Dama.
Muna addu’an Allah Ya jikan Danmajen Arewan Zazzau Injiniya Hayyatu Mustapha da rahamanSa, Ya yafe kurakkurenshi, ameen!!