An yi girgizar ƙasa mai ƙarfin maki 3.6 a Ghana

Hukumar da ke nazari kan yanayin ƙasa ta Ghana ta bayyana cewa girgizar ƙasar da aka a ranar lahadi ba ta wuce maki 3.6 a ma’aunin Ritcher ba.

Hukumar ta bayyana lamarin a matsayin wanda bai taka kara ya karya ba, tana mai bai wa mutane shawarar ci gaba da al’amuransu na yau da kullum.

“Motsin ƙasar kaɗan ne kuma ba a tunanin zai iya janyo wata matsala,” kamar yadda kamfanin dillancin labaran ƙasar Ghana ya ambato sanarwar hukumar tana cewa.

KU KUMA KARANTA: Girgizar ƙasa ta kashe mutane fiye da 100 a Nepal

Sanarwar da muƙaddashin shugaban hukumar, Isaac Kuuwan Mwinbelle, ya sanya wa hannu ta ce lamarin ya auku ne kilomita bakwai daga Weije a tsakiyar Accra da misalign karfe 7:17 na safiya.

An ji motsin a Nyanyano Kakraba, Weija, Pokuase, Adenta, Kanda da kuma wasu sassan tsakiyar Accra.

Hukumar ta ce za ta ci gaba da sa ido kan abubuwa tare da sanar da jama’a domin tabbatar da lafiyarsu.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *