An yi garkuwa da ma’aikatan simintin Ɗangote

0
71

’Yan bindiga sun yi garkuwa da ma’aikatam kamfanin simintin Ɗangote da ke yankin Okpella a Jihar Edo.

A ranar Litinin ne ’yan bindiga suka tare motocin ma’aikatan kamfanin a hanyar komawa gida bayan sun tashi aiki, inda suka yi awon gaba da su zuwa cikin daji.

An ce an sace su ne daga wata babbar bas ɗin ɗaukar ma’aikatan kamfanin kuma zuwa yanzu ba a tantance yawan wadanda abin ya rutsa da su ba.

Majiyoyi sun tabbatar cewa lamarin ya faru ne a Okpella, yankin da masana’antar simintin Ɗangote yake a Karamar Hukumar Etsako ta a Yamma a jihar.

KU KUMA KARANTA: An kama ƙasurguman masu garkuwa da mutane 33 a Nasarawa

Wani shaida a yankin ya ce, “mun samu labarin garkuwa da ma’aikatan kamfanin simintin Ɗangote a cikin wata bas ƙirar Coaster, amma ba mu san ko mutum nawa aka sace ba.

An yi ƙoƙarin samun ƙarin haske game da lamarin daga kakakin ’yan sanda na Jihar Edo, Chidi Nwabuzor, amma jami’in bai amsa sako da ƙiran ba.

Leave a Reply