An yanke wa wasu maza masu auren jinsi hukuncin ɗaurin shekara 100

0
14
An yanke wa wasu maza masu auren jinsi hukuncin ɗaurin shekara 100

An yanke wa wasu maza masu auren jinsi hukuncin ɗaurin shekara 100

An yanke wa wasu Amurka biyu masu auren jinsi hukuncin ɗaurin shekara 100 a gidan yari bayan samun su da laifin yi wa ‘ya’ya maza biyu da suke riƙo fyaɗe da kuma yaɗa bidiyon hakan da suka yi.

Mummunan lamarin na cin zarafi ya faru ne a kan yaran da ba su wuce shekara uku da kuma biyar ba.

Masu auren jinsin William mai shekara 34 da kuma Zachary Zulock mai shekara 36 za su ƙarasa rayuwarsu a gidan yari ba tare da yiwuwar yi musu afuwa ba, kamar yadda ofishin Babban Mai Shari’a na Gundumar Walton ya sanar.

“Ba shakka waɗannan mutane biyu sun yi wani mummunan abu mai ban tsoro tare da saka buƙatarsu a sama da komai da kowa,” in ji Babban Mai Shari’a Randy McGinley, kamar yadda kafar watsa labarai ta WSB-TV ta rawaito.

“Duk da haka, zurfin lalatar da waɗanda ake tuhuma suka yi, bai kai zurfin ƙoƙarin da wasu suka yi ba don tabbatar da cewa an yi hukunci na adalci. Dagiyar da na gani ta neman adalci a shekara biyun da suka wuce daga waɗannan yara da aka zalunta abu ne mai saka ƙarin gwiwa sosai, “in ji shi.

Yaran, waɗanda ‘yan’uwan juna ne da a yanzu suke da shekara 12 da 10, ma’auaratan ‘yan auren jinsi sun ɗauki riƙonsu ne daga wata ƙungiya ta Kirista da ke kula da yara masu buƙata ta musamman.

KU KUMA KARANTA: Kotu ta ɗaure ’yan canji 17 a gidan yari a Kano

‘Yan auren jinsin sun reni yaran a wata unguwa ta masu hali a wajen garin Atlanta. Suna da rufin asirinsu saboda shi Zachary ma’aikacin banki ne yayin da William ke aiki da gwamnati, amma bayan da wannan abu ya faru, sai aka gano wani mummunan sirri.

A bincikensu na faro a gidan mutanen, ‘yan sanda sun bibiyi wasu jerin bidiyoyi da kyamarorin gidan suka naɗa, waɗanda suka nuna yadda mutanen suka dinga cin zarafin yaran a wurare daban-daban a cikin gidan.

Shaidu sun nuna cewa har ma sun rika yi wa wasu abokansu alfahari da cin zarafin da suke wa yaran, kuma suna amfani da kafafen sada zumunta wajen yada bidiyoyi na azabar da wani gungun masu lalata da yara ke yi wa yara.

An kama masu auren jinsin ne a shekarar 2022 bayan da aka kama wani da ake zargin dan ƙungiyar tasu ne yana watsa abubuwan batsa na yara kuma ya bayyana wa masu bincike yadda su Zulock ke kirkirar bidiyon tare da yara maza da ke zaune a gidansu.

Dukansu Zulock sun amsa laifinsu – William a watan Agusta da Zachary a watan Oktoba na wannan shekara – kan tuhumar cin zarafin yara da lalata da luwadi da yara.

Bayan sauraron muhawara daga bangaren masu gabatar da kara da kuma masu ƙarar, alkali Jeffrey L Foster ya bi shawarar jihar inda ya yanke wa mutanen biyu hukuncin daurin shekaru 100 a gidan yari ba tare da yuwuwar sakinsu ba, lamarin da ke tabbatar da ɗaurin rai da rai a kansu.

Idan aka yi la’akari da tsananin laifin da suka aikata, babu wani daga cikinsu da zai cancanci a yi wa afuwa har sai sun cika shekaru 100 din nan, ko ma su mutu a gidan yari.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here