No menu items!

Sample Page Title

Date:

Babbar Kotun Jihar Kano ta yanke wa Geng Quangron hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan samunsa da laifin kashe kashe Ummita a Kano.

Antoni Janar na Jihar Kano Haruna Dederi ya tabbatar ƴan jarida da hukuncin kotun a ranar Talata.

A 2022 ne lamarin ya faru wanda ya yi matuƙar tayar da hankalin jama’a.

KU KUMA KARANTA: Ummul Khairi ta yi yunƙurin kashe ni bayan na tura mata sama da naira miliyan 60 – inji ɗan Chaina

A lokacin da lamarin ya faru, an zargi ɗan kasar Chainan da bin Ummulkusum Sani Buhari wadda aka fi sani da Ummita har gidansu da ke unguwar Janbulo inda ya soka mata wuka wanda hakan ya yi ajalinta.

Daga baya an gurfanar da Mista Geng a gaban kotu inda ya amsa laifin kisan Ummita tare da cewa ya kashe mata kuɗi sama da naira miliyan 60.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...