An wuce da gawar Muhammadu Buhari zuwa Daura, bayan sauka a filin jirgin sama na Katsina
An ɗauki gawar ne bayan an yi mata faretin girmamawa, inda wasu hafsoshin tsaron ƙasar suka ɗauki gawar daga jirgi, sannan suka raka ta zuwa jirgin da zai ɗauki gawar zuwa Daura inda za a binne ta.
A yanzu gawar tsohon shugaban na kan hanya zuwa Daura inda za a gudanar da sallar jana’iza da kuma binne ta.









