No menu items!

Sample Page Title

Date:

Rundunar ƴan sandan Najeriya reshen jihar Kano ta bayar da umarni ga manyan jami’anta kan su ƙara tsaurara tsaro a makarantun firamare da sakandare da kuma makarantun gaba da sakandare a jihar.

Wannan na zuwa ne bayan ƴan bindiga sun kwashe ɗalibai sama da 300 a Kaduna da kuma sace ɗalibai aƙalla 15 a Sokoto.

Mai magana da yawun ƴan sandan na Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa a ranar Talata ya fitar da sanarwa inda sanarwar ke cewa kwamishinan ƴan sandan jihar CP Mohammed Usaini Gumel ya bayar da umarni ga kwamandojin ƴan sanda na jihar da DPO-DPO da ke faɗin jihar kan su ƙara tsaurara tsaro a makarantun.

“A kan haka ne kwamishinan ‘yan sandan ya umarci kwamandojin da ke aiki da DPO-DPO su ƙara kaimi tare da mayar da hankali wurin sintiri a kewayen dukkan makarantun firamare da sakandare da na gaba da sakandare a faɗin jihar da ke cikin barazana,” in ji sanarwar.

KU KUMA KARANTA: ‘Yan bindiga sun sace ‘yan makarantar Allo a Sakkwato

“An ɗauki wannan matakin ne domin tabbatar da tsaro ga ɗalibai da malamai da sauran ɓangarorin ilimi a jihar. Manufar ƙara yawan jami’an ‘yan sanda a waɗannan wurare ita ce daƙile aikata laifuka da samar da ingantaccen yanayi mai dacewa don koyo da koyarwa,” kamar yadda sanarwar ta ƙara da cewa.

Matsalar tsaro na ƙara ƙamari musamman a arewacin Nijeriya inda a ƴan kwanakin nan ƴan bindigan suke kai hare-hare da dama.

Domin ko a tsakar daren Litinin sai da ‘yan bindigar suka sace aƙalla mutum 61 a ƙauyen Buda da ke Jihar Kaduna.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...