An tura matashi gidan yari kan yi wa jaririya fyaɗe

0
138

Kotu ta tisa ƙeyar wani matashi mai shekara 28 zuwa gidan gyaran hali kan yi wa jaririya ’yar wata tara fyaɗe.

Kotu ta ba da umarnin ne bayan Gwamnatin Jihar Legas ta gurfanar da matashin, bisa tuhume-tuhume guda biyu; lalata da kuma haifar da mummunar illa ga jaririyar.

Wanda ake tuhumar ya amsa laifin da ake tuhumarsa da shi.

Daga nan sai Mai Shari’a Rahman Oshodi ya tsare shi a gidan gyaran hali sannan ya dage shari’ar zuwa ranar 25 ga watan Maris don ci gaba da sauraren ƙarar.

KU KUMA KARANTA: Wani hedimasta ya yi wa ‘yar shekara shida fyaɗe

Tun da farko, lauyan jihar, Bukola Okeowo, ya shaida wa kotun cewa matashin ya aikata laifin ne a ranar 23 ga watan Maris, 2023 a yankin White Sand da ke Ijora, Badiya, a Jihar Legas.

Okeowo ya sanar da cewa wanda ake tuhuma ya yi wa jaririyar rauni da illa bayan yi mata fyaɗe.

Laifin, a cewarsa dai ya saɓa wa dokokin Jihar Legas na 2015 kuma duk wanda aka samu da laifin ana masa hukuncin ɗaurin rai da rai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here