An tsinci gawar yarinya Hanifa da ruwan sama ya tafi da ita a Zariya

0
0

An tsinci gawar yarinya Hanifa da ruwan sama ya tafi da ita a Zariya

Daga Idris Umar, Zariya

Gawar da aka shafe Kwanaki 6 ana nema an samu ganin ta ne a bayan Gyallesu ƙasan Kilaco a garin Zaria.

Baban Jami’in Kungiyar Red Cross shiyyar Zariya, Abdulmumin Adamu wanda ya sanar da haka a wata sanarwa, ya ce sun gano gawar ne da misalin ƙarfe 11:00 na safiyar Lahadi.

“Ranar 14 ga watan Satumba 2025 da misalin ƙarfe 11 na safe, mun samu gano gawar Haneefa a gangaren ƙasan Kilaco, a unguwar Gyallesu, Zariya.

“Hakan ya kawo ƙarshen bincike don ceto rayukan waɗanda ambaliyar ruwa ya yi awon gaba da su sakamakon gano dukkan gawawwakin da ake nema. ” Inji shi.

Idan za a iya tunawa, a ranar 8 ga watan Satumba 2025 ne wani mamakon ruwan sama da aka yi a unguwar Tudun Jukun dake gudumawar Tukur Tukur ya yi sanadiyar rasa rayukan wasu ɗalibai guda biyu, Fatima Sani Danmarke da Yusuf Surajo wanda aka fi sani da Abba.

A lokacin da aka ci gaba da neman gawar Haneefa wadda ita ce yayar ta Fatima ke goye da ita a lokacin da iftilain ya faru.

KU KUMA KARANTA: An tsinci gawar yaro da ruwa ya taho da shi a gadar Nahuta Potiskum

An dai cigaba da neman gawar Haneefa Yar shekara 3 tun faruwar al’amarin Amma Allah bai sa an ga gawarta ba sai a ranar lahadin nan.

Da yake tabbatar da gano gawar yarinyar Kakan yarinyar Mallam Suleiman da ke layin Adamu Mai Aljana, Magume ya tabbatar da ganin gawar Haneefa.

Yace mahaifin Haneefa Wanda Yaya ne ga mahaifiyar Fatima wadda ke goye da Haneefa lokacin da iftilain ya faru, yanzu haka ya tafi aikin Umrah tun ranar Jummaat.

Yace Mahaifin yana nan al’amarin ya faru kafin daga bisani ya tafi aikin Umrah.

Yace “A yau ranar lahadi da safe a ka kira ni aka shaida min cewa an ga gawar Haneefa.

“Wadanda suka gan ta sunce wata bishiya ce ta tare gawar achan bayan Gyallesu Zaria.

“Don haka nan da nan muka shirya sallar Jana’iza daga bisani Kuma aka yi mata sutura aka binne ta.

Mallam Suleiman ya kara da cewa dama tun a shekaran jiya an gudanar mata da Salatul Gaib, ( Sallar gawar da baa gan ta ba) bayan sallar Magrib a Masallacin Mallam Isa cikon kwami dake magume.
Inji shi.

Alhaji Sani Danmarke sai yayi godiya ga dukkan wadanda suka bada gudumawa wajen kokarin gano yaran da ruwa ya tafi dasu.

Yayi adduar Allah Ya sakawa kowa da alheri bisa nuna alhini da jama’a suka yi kan wannan iftilai da ya same su

Yanzu haka limaman masallatai na ci gaba da wayar da kan al’umma game da yadda lamarin ya wakana don kaucewa faruwar irin hakan.

Limaman suna kira ga masu ababen hawa da masu yara ƙanana da su kiyaye duk lokacin da aka yi ruwa mai yawa su daina faɗa mashi yayin da suke tafiya su kuma iyaye susa idanu a duk lokacin da akayi ruwa mai ƙarfi.

Leave a Reply