No menu items!

Sample Page Title

Date:

Babbar Kotun Jihar Kano ta tsare tsohon Manajan-Daraktan Hukumar Kayayyakin Noma ta jihar (KASCO), Bala Muhammad Inuwa kan zargin satar naira biliyan 3.2 daga asusun gwamnatin jihar.

Kotun ta ba da umarnin tsare shi ne a yayin ci gaba da sauraron shari’ar da ake zargin shi da ɗansa aikata laifuka 10 da suka danganci raba wa muƙarrabansu naira biliyan 3.2.

Lauyan gwamnatin jihar, Zaharadeen Hamisu Kofar Mata, ya ce masu gabatar da ƙara sun mika wa kotun gamsassun hujjoji da shaidun da ya kamata, domin ta hukunta waɗanda aka zargin.

Ya kuma ƙalubalanci buƙatar lauyan waɗanda ake ƙara, Farfesa Nasiru Adamu Aliyu, na nema beli.

KU KUMA KARANTA: Kotu ta bada umarnin gurfanar da tsohon shugaban KASCO kan zargin damfarar naira biliyan huɗu

Sai dai a martaninsa, Farfesa Nasiru ya ce, lauyan masu ƙara da neman a hukunta waɗanda ake zargi ba tare an bi tsarin da ya dace ba, don haka ya buƙaci kotu kada ta biye wa ɓangaren masu kara.

Bayan sauraron ɓangarorin ne alkalin kotun, Mai Shari’a Hafsat Sani Yahya ta bayyana cewa masu kara sun gabatar da wadatattun shaidu da hujjoji da za a iya ci gaba da shari’ar.

Don haka ta buƙaci lauyan wanda ake ƙara ya ƙara shigar da bukatar neman beli, wanda ta ce za ta karɓa.

Daga nan ta ɗage zaman zuwa ranar 6 ga watan Disamba, 2023.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...