Ma’aikatar ilimi ta rufe Makarantar Firameren Great Leaders International kan zargin mai makarantar da yi wa ɗaliba mai shekaru huɗu fyaɗe.
Da take sanar da rufe makarantar da ke yankin Ime-Obi, Agbor a Ƙaramar Hukumar Ika ta Kudu ta Jihar Delta, ma’aikatar ilimin jihar ta yi tir da ɗanyen aikin a matsayin “rashin imani da tsabar kidahumanci.”
“’Yan sanda na tsare da wanda ake zargin, wato mai makarantar, domin ya girbi abin da ya shuka a matsayin izina ga masu irin halinsa,” in ji ma’aikatar.
Sanarwar da Babban Sakataren Ilimin ma’aikatar, Augustine Oghoro, ya fitar ta bayyana takaici bisa yadda malamin da aka ba wa kula da tarbiyya da ilimantar da ƙananan yara zai yi irin wannan aikin ashsha.
Ya ƙara da cewa Great Leaders International na daga cikin haramtattun makarantun da ke jihar, kuma ma’aikatar ta daɗe da rufe ta.
KU KUMA KARANTA: An yanke wa shugaban cibiyar kula da lafiya ɗaurin rai-da-rai kan yi wa wata yarinya fyaɗe
Rundunar ’yan sandan jihar ta tabbatar da tsare wanda ake zargin tare da cewa tana gudanar da bincike kan lamarin.
Ma’aikatar ilimin ta gargaɗi iyaye kan cin mutuncin malamai saboda horas da ’ya’yansu.
Babban Sakatarenta, Augustine Oghoro, ya yi gargaɗin ne a yayin da yake batu kan yadda iyayen ɗalibai a wata makarantar sakandaren gwamnati suka kai wa malamin da ya ladabtar da ɗansu a hari, inda ta hakan suka yi ajalin malamin.
Irin haka ta kuma faru a watan Oktoba a Makarantar Sakandaren Ehwerhe da ke Agbarho, inda wani mahaifi ke jagorantar gungun wasu ɗalibai da ke hana malamai da sauran ɗalibai sakat.