An tone kabari, an sace gawa a maƙabarta a Yobe — ‘Yansanda sun fara bincike

0
404
An tone kabari, an sace gawa a maƙabarta a Yobe — 'Yan sanda sun fara bincike

An tone kabari, an sace gawa a maƙabarta a Yobe — ‘Yansanda sun fara bincike

Rundunar ‘yansandan jihar Yobe ta fara bincike bayan gano wani kabari da aka tone, sannan aka sace gawar da ke ciki a makabartar unguwar Makwalla da ke garin Jakusko.

A cewar wata sanarwa daga Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar, SP Dungus Abdulkarim, ta ce wani mazaunin garin ne ya kai rahoton lamarin ga sashen ‘yansandan Jakusko a ranar Laraba, 13 ga Nuwamba, 2025.

Bayan samun rahoton, wata tawagar jami’ai tare da haɗin gwiwar shugabannin al’umma sun ziyarci maƙabartar kuma sun tabbatar da cewa an tone kabarin kuma an cire gawar da ke ciki. Har zuwa yanzu ba a san waɗanne mutane ne suka yi wannan ɗanyan aikin ba, amma ‘yansanda sun fara bincike.

‘Yansanda sun ƙara sa ido sosai kuma sun fara bincike mai zurfi, gami da duba wasu kaburbura a yankin don hana ƙarin aukuwar hakan nan gaba.

Da yake mayar da martani ga lamarin, Kwamishinan ‘yansanda, CP Emmanuel Ado, ya bayyana wannan aiki a matsayin “mai cin naman mutane, mai mugunta, kuma babban keta mutuncin ɗan’adam da cin zarafin tsarkin matattu.” Ya yi alƙawarin cewa waɗanda ke da alhakin za su fuskanci cikakken nauyin doka da zarar an kama su.

KU KUMA KARANTA: Zanga-zanga ta ɓarke akan ginin maƙabarta a Legas

Rundunar ‘yansanda ta yi kira ga mazauna yankin da su inganta tsaron maƙabarta a faɗin jihar tare da yin kira ga jama’a da su kai rahoton duk wani abu da ake zargi ko kuma wani mutum kusa da maƙabarta.

Neptune Prime Hausa

Leave a Reply