No menu items!

Sample Page Title

Date:

An tarwatsa masu zanga-zanga kan ƙoƙarin kunna wuta a ƙofar gidan gwamnatin Kano

Wasu daga cikin masu zanga-zangar adawa da wahalhalun da ake fama da su a faɗin ƙasar nan sun kunna wuta a kofar gidan gwamnati da ke Kano a safiyar ranar Alhamis.

Masu zanga-zangar daga sassa daban-daban na birnin sun yi dandazo ne a gidan gwamnati, inda gwamna Abba Kabir Yusuf zai yi musu jawabi.

Sai dai wasu daga cikinsu sun haɗa tayoyi suka banka musu wuta a lokacin da suke tunkarar ƙofar gidan gwamnatin.

KU KUMA KARANTA: Ana gudanar da zanga-zanga kan tsadar rayuwa a Najeriya

Hakan ya sanya jami’an tsaro a gidan gwamnati suka harba barkonon tsohuwa domin tarwatsa masu zanga-zangar.

Masu zanga-zangar sun tsere inda suka nufi hanya daban-daban cikin ruɗani.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...