An taƙaita wuraren da masu zanga-zanga za su bi a Abuja

0
59
An taƙaita wuraren da masu zanga-zanga za su bi a Abuja

An taƙaita wuraren da masu zanga-zanga za su bi a Abuja

A yayin da aka shiga yau Alhamis 1 ga watan Agusta da ake sa ran fara zanga-zangar adawa da matsin rayuwa a Najeriya, wadda gwamnati ta yi ta kiraye-kirayen a fasa, wata Babbar Kotun Birnin Tarayya Abuja ta taƙaita wa masu zanga-zangar amfani da ko ina sai filin wasa na MKO Abiola da ke babban birnin ƙasar kawai.

Mai shari’a Sylvanus Oriji ne ya bayar da wannan umarni a jiya Laraba yayin da yake yanke hukunci a bisa wata takardar bukatar da Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT) Nyesom Wike ya gabatar a gaban kotun.

A cikin takardar neman izinin da lauyansa, Ogwu Onoja ya gabatar, Minista Wike ya nemi a ba da umarnin dokar wucin gadi da ta haramta wa shugabanni biyar na zanga-zangar taruwa ko yin fito-na-fito a kan duk wata hanya da tituna da ofisoshi, da wuraren taron jama’a a cikin babban birnin tarayya Abuja, daga tsakanin 1 zuwa 10 ga Agusta, ko kuma wata rana bayan haka.

KU KUMA KARANTA: Ba ku da damar ta da zaune tsaye a Najeriya – Akpabio ga masu zanga-zanga

Ya kuma nemi da a sake ba da umarni na wucin gadi da ya umurci jami’an tsaro su hana shugabannin da ke zanga-zangar taruwa ko yin fito-na-fito a duk wata hanya, ofis, ko wuraren jama’a da ke cikin babban birnin tarayya Abuja a tsakanin ranakun 1 zuwa 10 ga watan Agusta, har zuwa lokacin da za a ci gaba da sauraron karar da ya shigar.

Ministan wanda ya ce Gwamnatin Tarayya ba ta ƙyamaci wannan zanga-zangar ba, ya yi iƙirarin cewa bayanan sirri da tsaro da suka samu sun nuna cewa wasu daga cikin shugabannin zanga-zangar na da niyyar yin amfani da ita don haifar da ɓarnar da ba za ta iya kwatantuwa ba a wuraren jama’a da toshe hanyoyin mota don hana zirga-zirgar mutane da ababen hawa da kuma kawo cikas ga zaman lafiyar al’umma.

Don haka ya umarci waɗanda ake ƙarar daga na ɗaya zuwa na biyar da su yi amfani da filin wasa na Moshood Abiola kawai don zanga-zangar.

A halin da ake ciki, kotun ta ba da umarnin gudanar da dukkan sharuɗan da ta sanya a cikin ƙarar tare da bayar da umarnin tsare wadanda ake ƙara ta hanyar sanya haka a jaridu.

Wadanda Wike ya shigar da ƙarar tasu da ake tuhuma su ne Omoyele Sowore da Damilare Adenola da Adama Ukpabi da Tosin Harsogba da kuma wasu mutane da ba a san su ba.

Sauran masu ƙara a shari’ar sun haɗa da sufeto-Janar na ‘yan sanda da kwamishinan ‘yan sanda na Abuja da Darakta Janar na hukumar tsaro ta farin kaya da Darakta Janar na hukumar tsaro ta Civil Defence da shugaban hafsan so da babban hafsan sojin sama da kuma babban hafsan sojojin ruwa.

Leave a Reply