No menu items!

Sample Page Title

Date:

An ceto 1 daga cikin ‘yan matan Chibok, an miƙa ta ga gwamnatin Borno

Shugaban Rundunar Operation haɗin kai a Arewa maso Gabas, Maj.-Gen. Waidi Shuaibu, ya miƙa wata ‘yar Chibok da aka ceto, Ihyi Abdu, ga Gwamnatin jihar Borno.

Ya zuwa yanzu dai an ceto ƴan matan Chibok 19 ta hanyar ɓarin wutar sojiji. Manjo Shuaibu ya jaddada ci gaba da ƙoƙarin Sojojin na ceto sauran ‘yan matan da ke hannun mayaƙan Boko Haram.

Yayin bayyana yadda aka ceton tsohuwar ɗalibar, Manjo Haruna, wanda ke riƙe da muƙamin shugaban runduna ta 7, ya yi bayani cewa an ceto Ihyi Abdu, tare da ‘ya’yan ta guda biyu, a ranar 23 ga Yuni yayin wani farmaki a dajin Sambisa.

KU KUMA KARANTA: An ceto wani jariri da aka kashe mahaifiyarsa a wani mummunan farmaki ta sama a Gaza

Ihyi, yanzu ta zama mai shekara 27, an yi garkuwa da ita a shekarar 2014 kuma an tilasta musu aure da ‘yan Boko Haram, wanda ta zauna tare da shi a Garin Mustapha a cikin dajin Sambisa.

A halin yanzu, tana ɗauke da juna biyu na watanni uku kuma ta samu cikakken binciken lafiya tare da ‘ya’yan ta tun bayan ceto su.

Bugu da ƙari, an miƙa mutum 330 da aka ceto, wanda suka haɗa da mata 110 da Yara 220, ga gwamnatin Jihar Borno.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...