An soke wasannin da Taylor Swift za ta yi i a Austria

0
96
An soke wasannin da Taylor Swift za ta yi i a Austria

An soke wasannin da Taylor Swift za ta yi i a Austria

Kamfanin Dillancin Labarai na AP ya ruwaito cewa da yawa daga cikin masoyan nata sun kashe dubban kuɗaɗen Euro wajen yin tafiya da kama otel da kuma abinci.

Masoyan Taylor Swift sun nuna rashin jin daɗinsu bayan da aka soke wasannin da mawaƙiyar za ta yi guda uku waɗanda tuni an kammala sayar da tikitinsu a Austria.

Soke wasannin ya biyo bayan bayanan sirri da hukumomin tsaro suka ce sun gano waɗanda ke cewa akwai a kai harin ta’addanci a birnin Vienna.

Da yawa daga cikin masoyanta sun ɗunguma zuwa shafukan sada zumunta don nuna rashin jin daɗinsu kan soke wasannin mawaƙiyar ta Amurka ‘yar asalin jihar Pennsylvania.

KU KUMA KARANTA;Ruwan sama ya lalata gidaje da dama a garin Faguji, jihar Bauchi

Wasu masoyan nata sun bayyana yadda suka kwashe watanni suna shirin halartar wasannin har ma suka ware wasu kaya na musamman da za su saka a lokacin.

Kamfanin Dillancin Labarai na AP ya ruwaito cewa da yawa daga cikin masoyan nata sun kashe dubban kuɗaɗen Euro wajen yin tafiya da kama otel da kuma abinci.

Hukumomi sun ce sun kama mutum biyu masu tsatstsauran ra’ayi, inda ɗayansu ya amsa yin mubaya’a ga ƙungiyar IS mai iƙirarin jihadi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here