An shiga damuwa bayan sojoji sun ɗage zaɓen shugaban ƙasa a Mali

0
322

Mahukunta a Mali sun ɗage zaɓen shugaban ƙasar da aka tsara tun farko za a yi a watan Fabrairun 2024.

Mai magana da yawun gwamnatin ƙasar, Abdoulaye Maiga ne ya bayyana wasu gyare-gyare da za a yi wa tsarin mulkin ƙasar da kuma dokokin zaɓe a matsayin dalilan da suka janyo ɗage zaɓen.

A cikin wata sanarwa da ya fitar, Abdoulaye Maiga ya ce “An ɗage zaɓukan da a baya aka tsara gudanarwa a ranar 4 da kuma 18 ga watan Fabrairun 2024 saboda dalilan yin gyare-gyare.

Ya ce dalilan sun haɗa da batun amincewa da sabon kundin mulkin ƙasar da kuma gyaran fuska ga dokokin zaɓe.

Gamayyar ƙungiyoyin fararen hula da jam’iyyun adawa sun bayyana rashin jin daɗinsu a kan wannan sanarwa.

KU KUMA KARANTA: Faransa za ta janye jakadanta a jamhuriyar Nijar

Tun da farko, shugaba Assimi Goita ya nemi a gudanar da zaɓen ne a shekara ta 2026, daga baya kuma ya janyo shi zuwa 2025 bayan fuskantar matsin lamba daga ƙungiyar Ecowas.

A watan Afrilun 2021 ne dai, gwamnatin mulkin sojan Mali ta ba da tabbacin gudanar da zaɓe cikin watan Fabrairun 2024.

Cibiyar tsara dabarun mulki ta Afrika ta ce yanayin tsaro na ƙara taɓarɓarewa a Mali tun bayan da gwamnatin mulkin sojin ta fara yanke hulɗa da ƙasashen duniya, da kuma dakarun Majalisar Ɗinkin Duniya.

Juyin mulki biyu da Mali ta yi fama da su, suna da alaƙa da gazawar hukumomi wajen magance rikicin ‘yan ta-da-ƙayar-baya da masu iƙirarin jihadi da ya yaɗu a Afirka ta Yamma cikin shekara 10 da ta wuce.

Yanayin tsaro ya ƙara ƙazancewa a Mali saboda rikici tsakanin ƙungiyoyi biyu masu ɗauke da bindiga.

Ba a san martanin da ƙungiyar Ecowas za ta mayar ba, game da wannan sanarwa ta shugabannin mulkin sojan na Mali.

Leave a Reply