No menu items!

Sample Page Title

Date:

Daga Ibraheem El-Tafseer

A wani lamari mai ta da hankali, an tsinci gawar ‘yar wani ɗan majalisar dokokin jihar Borno mai wakiltar Ngala, Bukar Abacha an shaƙe mata wuya ta mutu har lahira a gidansu na Gidan Dembe da ke Maiduguri. kamar yadda kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya ya ruwaito.

Mijin matar da abin ya shafa, cikin baƙin ciki, ya tarar da gawarta babu rai tare da an ɗaure hannayenta da ƙafafunta a bayanta, yayin da yaronsu ɗan shekara biyu yana ta kuka.

Mummunan lamarin ya faru ne a ranar Talata, 17 ga Oktoba, 2023, kuma nan take rundunar ‘yan sanda ta Gwange, ta kai gawar marigayiyar zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri domin a duba gawar da kuma ci gaba da bincike. An bar al’umma cikin alhini, tare da neman a gaggauta gudanar da bincike mai zurfi don bayyana gaskiyar da ke tattare da wannan mummunan laifi.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...