An sauya Kwamishinan ’yan sandan Kano
Sabon kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, Salman Dogo Garba, ya fara aiki tare da bada tabbacin a shirye ya ke na tabbatar da ingantaccen tsaro na rayuka da dukiyoyi.
Da yake jawabi a wajen bikin bankwana da aka gudanar a jami’ar Mess Bompai Kano wanda aka shirya domin karrama tsohon kwamishinan ‘yan sanda, Husani Gumel, wanda aka ƙara masa girma zuwa AIG, sabon CP ya nemi goyon baya da haɗin kai ga jami’ai da maza na rundunar ‘yan sandan Kano da kuma haɗin kai jama’a.
A nasa jawabin, CP mai barin gado ya yabawa hafsa da jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Kano bisa gagarumin goyon bayan da suka ba shi a lokacin da yake riƙe da muƙamin CP, inda ya jaddada cewa hakan ne ya sanya ya samu nasara a Kano.
AIG Gumel ya buƙaci da su baiwa sabon CP duk goyon bayan da ake buƙata domin samun damar cimma manufofin da aka sa gaba.
A yayin bikin mai ban sha’awa, ƙungiyar ‘yan jarida ta kasa reshen jihar Kano, ta bayar da lambar yabo ga CP mai barin gado bisa ga irin kwazon da ya nuna a lokacin da yake rike da muƙamin.
KU KUMA KARANTA: An umarci ƴan sanda su tsaurara tsaro a makarantun Kano
Muhimman abubuwan da suka faru sun haɗa da bayar da kyautuka ga jami’an ‘yan sanda da maza da sauran masu hannu da shuni bisa jajircewarsu wajen samar da zaman lafiya a jihar.