An sanya dokar taƙaita zirga-zirga a ƙananan hukumomin da za a yi zaɓen cike gurbi a Kano 

0
189
An sanya dokar taƙaita zirga-zirga a ƙananan hukumomin da za a yi zaɓen cike gurbi a Kano 

An sanya dokar taƙaita zirga-zirga a ƙananan hukumomin da za a yi zaɓen cike gurbi a Kano

Daga Jameel Lawan Yakasai

Rundunar ’yansandan jihar Kano, ta ce ta ɗauki matakan da suka dace tare da haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaro domin tabbatar da gudanar da ƙarasa zaɓen ɗan majalisa na Ghari/Tsanyawa da na cike gurbin majalisar jiha a Bagwai/Shanono cikin lumana, gaskiya, adalci da inganci, a ranar Asabar 16 ga Agusta, 2025.

Wannan na cikin sanarwar da kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar a ranar Alhamis.

KU KUMA KARANTA: INEC ta sanya ranar 16 ga Agusta don zaɓen cike gurbi a mazabu 16

Sanarwar ta bayyana cewa an sanya dokar taƙaita zirga-zirgar motoci, Adaidaita Sahu da babura daga ƙarfe 12:00 na tsakar dare Juma’a 15 ga watan zuwa ƙarfe 6:00 na yammacin ranar Asabar 16 ga watan, tare da banbance motocin da ke kan ayyukan gaggawa irin su motar asibiti, motar kashe gobara, da motocin ma’aikatan zaɓe da masu sa idanu na hukuma.

Haka kuma sanarwar ta nuna cewa masu kada kuri’a kaɗai da aka tantance aka yarda su shiga rumfunan zaɓe, tare da haramta ɗaukar makamai, sanya kayayyakin da ke ɗauke da tambarin jam’iyyun siyasa, ko yawo a kusa da wuraren kada kuri’a.

Rundunar ta kuma hana ƙungiyoyin tsaron jiha irin su ’yan sa kai da jami’an KAROTA shiga rumfunan zaɓe.

Kwamishinan ’yan sandan ya tabbatar da cewa hukumomin tsaro za su kasance masu adalci, da bin ƙa’ida, tare da kira ga mazauna da baƙi a yankunan da za a yi zaɓe su haɗa kai wajen ganin an gudanar da zaɓen cikin nasara.

Leave a Reply