An samu tashin farashin kayan masarufi mafi muni a Najeriya cikin shekara 27 – Hukumar ƙididdiga

0
213

Daga Ibraheem El-Tafseer

A Najeriya al’umma na kokawa kan tsadar rayuwa da tashin farashin kayan abinci, tun bayan da shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu ya hau mulki watanni takwas da suka gabata.

Lamarin dai ya yi ƙamarin da ya sa wasu daga cikin al’ummar ƙasar suka fara gudanar da zanga-zanga a wasu daga cikin jihohin kasar.

A ranar litinin, al’umma sun hau kan titunan birnin Minna na jihar Neja da ke arewa maso tsakiyar ƙasar suna zanga-zanga kan matsin rayuwa.

Ɗaya daga cikin masu zanga-zangar ta shaida wa BBC cewar: “Ba mu iya cin rabin abin da muke ci a baya, komai ya yi tsada, maza na tserewa (su bar iyalai) ba a sake ganin su…aure na mutuwa saboda rashin abinci.”

An dai zaɓi shugaba Tinubu ne da tunanin samun sauƙi kan wahalhalun da al’ummar ƙasar suka faɗa ciki tun a lokacin tsohon shugaban ƙasar Muhammadu Buhari.

KU KUMA KARANTA: Me ke kawo hauhawan farashin kayan abinci a kowane mako a Najeriya?

Mutane da dama sun kyautata wa Tinubu zato, ganin cewa ya mulki jihar Legas, cibiyar kasuwanci da tattalin arziƙin ƙasar tsawon shekara takwas a matsayin gwamna.

Kuma har gobe shugaban ƙasar na bugun ƙirjin cewa shi ne ya ɗora jihar kan turbar bunƙasar tattalin arziƙi da take cin gajiya a yanzu.

Sai dai watanni da dama bayan hawan sa kan mulki, mutane da dama sun fara karaya ganin cewa abubuwa na ƙara taɓarɓarewa game da halin rayuwa.

Alƙaluman da Hukumar ƙididdiga ta Najeriya ta fitar a watan Janairu sun nuna cewa an samu tashin farashi mafi muni a ƙasar cikin shekara 27.

Hukumar ta ce tashin farashi ya ƙaru da kashi 28.92% a watan Disamban 2023, lamarin da ke nuna cewa an kwashe shekara guda ana samun tashin farashi a jere a ƙasar.

Wani abu da ke ƙara jefa mutanen ƙasar cikin damuwa shi ne hali na rashin tabbas kan lokacin da abubuwa za su daidaita.

Leave a Reply