An samu rahoton ɓullar wata cuta mai alaƙa da gurɓataccen ruwa a Dubai

0
114

Mutane ƴan ƙalilan ne a ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa UAE suka nuna alamun wata cuta da ake zargin tana da alaƙa da gurɓataccen ruwa, bayan ruwan sama mai ƙarfin gaske da aka yi wanda ya haifar da ambaliya a makon jiya, a cewar Ma’aikatar Lafiya ta ƙasar.

Sai dai a sanarwar da kamfanin dillancin labarai ta ƙasar ta fitar a ranar Laraba, ba ta bayyana takamaiman adadin mutanen da suka kamu da cutar ba, da kuma iri maganin da aka ba su.

”Ba a samu alƙaluma masu yawa ba kan mutanen da suka nuna alamun kamuwa da cutar wadda ke da alaƙa da gurɓataccen ruwa”, kuma suna samun kulawa daga asibiti, a cewar ma’aikatar.

Kana ba ta bayyana wacce irin cuta ce ta gurbata ruwan ba.

KU KUMA KARANTA: Ambaliyar ruwa ta kawo gagarumin tsaiko a sufurin jiragen sama a Dubai

A ranar 16 ga watan Afrilu ne aka tafka ruwan sama mai ƙarfin gaske a ƙasar ta Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, wanda ya haifar da tsaiko ga wasu sassan kasar ta yankin Gulf, lamarin da ya yi sanadiyar mamaye wasu birane da suka haɗa da Dubai da kuma yankunan arewacin ƙasar.

Ma’aikata uku ƴan kasar Philippines sun mutu sakamakon ambaliyar ruwa a Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa.

Wasu mata biyu ne suka mutu a cikin motarsu yayin ambaliyar, sannan wani mutum da ya mutu a lokacin da motarsa ta faɗa cikin wani rami, kamar yadda ma’aikatar kula da baƙi ta Philippines ta sanar.

Jimillar mutanen da suka mutu sun kai hudu idan aka hada da wani dattijo mai shekara 70 da ruwan ya tafi da shi a cikin motarsa a Ras Al-Khaimah, daya daga cikin masarautun yankin Gulf guda bakwai mai arzikin man fetur.

Leave a Reply