An samu arangama tsakanin sojoji da wasu mutane a Mangu da ke Filato

Daga Ibraheem El-Tafseer

Rahotonni daga Yankin ƙaramar Hukumar Mangu da ke jihar Filato na cewa an samu wata arangama tsakanin sojoji da wasu mutane a yankin.

Lamarin ya faru ne da safiyar ranar Asabar, lokacin da jami’an tsaron ke ƙoƙarin wanzar da zaman lafiya a yankin.

Wata majiya a yankin da ta buƙaci a sakaya sunanta ta shaida wa BBC cewa an samu arangamar ne tsakanin jami’an tsaro da ‘yan ƙabilar Magabul a yankin ƙaramar hukumar Mangu.

Majiyar ta ce an samu asarar rayuka, sai dai ba ta bayyana adadin mutanen da suka rasun ba.

To sai dai shugaban matasan ƙaramar hukumar, wanda ta tabbatar wa da BBC faruwar lamarin, ya ce babu asarar rai, ko guda, sai dai ya ce har yanzu yana kan tattara bayanai.

KU KUMA KARANTA: An cafke waɗanda suka kitsa kashe-kashen Filato

Arangamar na zuwa ne bayan da gwamnan jihar Caleb Mutfwang ya sassauta dokar hana fita ta tsawo kwana guda da aka sanya a yankin.

Gwamnan ya ce ya sassauta dokar ne inda ya mayar da ita daga ƙarfe takwas na safe zuwa huɗu na maraice sakamakon ci gaban zaman lafiya da aka samu a yankin.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *