An samu ƙarin gawarwaki a tashin bama-bamai a Somaliya

0
219

Ma’aikatan agajin gaggawa a tsakiyar Somaliya sun tona baraguzan gine-gine domin ƙwato wasu gawarwaki jiya Lahadi bayan da wata motar ɗaukar kaya ta kashe mutane sama da goma tare da ruguza gine-gine.

Wani ɗan ƙunar baƙin wake ne ya tuƙa motar da ke ɗauke da ababen fashewa zuwa wani shingen binciken jami’an tsaro a garin Beledweyne a ranar Asabar ɗin da ta gabata, lamarin da ya haifar da fashewar wani abu da ya sa mutane da dama suka maƙale a ƙarkɓashin bulo da siminti.

‘Yan sanda sun shaida wa kamfanin dillancin labaran AFP a ranar Lahadin da ta gabata cewa adadin waɗanda suka mutu ya haura mutane 13 da aka ruwaito tun farko amma ba su iya bayar da takamaiman adadi ba.

KU KUMA KARANTA: Sojojin Nijar sun amince su tattauna da ECOWAS

Mataimakin kwamandan ‘yan sandan Beledweyne Sayid Ali ya ce, “Ana gudanar da bincike da share wurin da fashewar ta auku, an kuma gano gawarwakin da safiyar ranar Litinin a ƙarƙashin baraguzan gine-gine.”

“Akwai fargabar adadin waɗanda suka mutu na iya ƙaruwa,” in ji shi, ya ƙara da cewa ɗan ɓunar baƙin waken ya auna wata unguwa mai cike da hada-hadar jama’a da ke ɗauke da kasuwanci da gine-gine.

Shugaban Somaliya Hassan Sheikh Mohamud ya jajantawa harin, inda ya ninka alƙawarinsa na “kawar da” ‘yan ta’addar Al-Shabaab da suka yi ta tayar da ƙayar baya ga gwamnatin tsakiyar ƙasar mai rauni sama da shekaru 15.

“Irin haka lamarin ba zai taɓa hana mu ci gaba da kawar da ‘yan ta’adda ba,” in ji shi. Babu wani da’awar kai harin bam na ranar Asabar, wanda ya zo bayan da gwamnatin Somaliya ta amince da cewa ta fuskanci ” koma baya da dama” a yaƙin da take da ‘yan ta’adda masu alaƙa da Al-Qaeda.

Wani jami’in ‘yan sandan yankin Ahmed Yare Adan ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa a ranar Asabar cewa harin ya yi sanadiyar mutuwar mutane 13 tare da jikkata 45.

Mataimakin ministan kiwon lafiya na Somaliya Mohamed Hassan ya faɗa a yammacin jiya Asabar cewa “kusan mutane 13 da suka samu munanan raunuka (an kwashe) daga Beledweyne a daren” kuma an kawo su Mogadishu babban birnin ƙasar don yi musu magani.

Mohamud ya hau karagar mulki a watan Mayun bara yana mai shan alwashin cewa zai yi yaƙi da Al-Shabaab, waɗanda aka fatattake su daga Mogadishu a shekarar 2011 amma har yanzu suna riƙe da yankunan karkara.

Dakarun Tarayyar Afirka da aka tura Somaliya a shekara ta 2007 tare da wa’adin watanni shida amma har yanzu suna nan a ƙasa.

Ƙudurorin Majalisar Ɗinkin Duniya sun buƙaci a rage yawan dakarun wanzar da zaman lafiya a Somalia a ƙarshen shekara mai zuwa, inda za su miƙa tsaro ga sojojin ƙasar da ‘yan sandan Somalia.

Leave a Reply