No menu items!

Sample Page Title

Date:

Shugaban ƙaramar hukumar Akwanga da aka sace a Jihar Nasarawa, Safiyanu Isah Andaha, tare da wasu mutum uku sun kuɓuta bayan an biya kuɗin fansa miliyan 10.

An sace shugaban tare da abokinsa, Adamu Custom da wasu mutum biyu, a kan titin Akwanga zuwa Andaha a daren Litinin.

Wani makusancin shugaban ƙaramar hukumar, wanda ya buƙaci a sakaya sunansa, ya shaida wa Aminiya cewa an sako duk waɗanda abin ya shafa ne bayan an biya kuɗin fansa.

Majiyar ta ce “An sake su ne a daren Talata da misalin karfe 9 a bayan wani gidan mai da ke kan titin Bayan Dutse, kuma an biya kuɗin fansa naira miliyan 10.”

KU KUMA KARANTA: ‘Yan bindiga sun sace shugaban ƙaramar hukuma tare da jama’arsa

Majiyar ta ce shugaban ƙaramar hukumar ya bayyana cewa maharan suka ci zarafinsu lokacin da suka sace su.

Aminiya ta samu labarin cewa jim kaɗan bayan sakin su aka garzaya da su zuwa Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya (FMC), da ke Keffi don duba lafiyarsu.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...