An sako malamin addinin Kiristan Jamus da aka yi garkuwa da shi a Mali

0
165

Waɗanda suka yi garkuwa da malamin addinin kiristan nan ɗan ƙasar Jamus, Hans Joachim Lohrem a Bamako babban birnin Mali a shekarar da ta gabata, sun sakoshi.

Patient Nshombo wani jami’in majami’ar ne ya tabbatar wa Kamfanin Dillancin Labaran Reuters, labarin sako babban malamin addinin Kiristan.

“Kwarai an sako shi, amma ya kamata mu jira ƙarin bayani daga hukumomi.”

Sai dai hukumomin Mali da kuma mai magana da yawun ofishin harkokin ƙasashen wajen Jamus, ba su ce komai dangane da lamarin ba.

KU KUMA KARANTA: Yara miliyan 2.2 a Jamus na cikin haɗarin talauci

Malamin majami’ar da ya kwashe shekaru 30 ya na zaune a Bamako, a shekarar da ta gabata ce dai aka sace shi a lokacin da ya ke shirin gudanar da wani babban taro, inda aka nemeshi aka rasa duk da anga motarsa a kofar gidansa amma kuma wayarsa a kashe.

Tun bayan da aka sace malamin, babu wani ko wata ƙungiya da ta ɗauki alhakin aikata hakan akansa, duk da cewar ana yawan samun matsalar satar baki ‘yan ƙasashen ƙetare a ƙasar ta Mali da ke fama da matsalar tsaro.

Leave a Reply