An saki ‘yan Koriya ta Kudu da aka sace a Najeriya

0
136

‘Yan bindiga sun saki ‘yan ƙasar Koriya ta Kudu guda biyu da suka yi garkuwa da su a farkon watan nan a yankin Neja Delta na Najeriya, a cewar wata sanarwa da Ma’aikatar harkokin wajen Koriya ta fitar a yau Asabar.

Ranar 12 ga watan Disamba, ‘yan bindiga suka yi wa tawagar ‘yan Koriya ta Kudu kwanton-ɓauna inda suka kashe sojoji huɗu da ke tsaron lafiyarsu da kuma direbobinsu biyu sannan suka yi garkuwa da su.

Mutanen biyu ma’aikatan babban kamfanin gine-gine ne na Koriya ta Kudu mai suna Daewoo Engineering & Construction Co, a cewar kamfanin dillancin labarai na Yonhap da ke Seoul.

Sai dai a sanarwar da Ma’aikatar Harkokin Wajen ta fitar ta ce an saki mutanen ba tare da ko ƙwarzani ba.

KU KUMA KARANTA: Kotun Ƙolin Najeriya ta hana sakin shugaban IPOB Nnamdi Kanu

“Ranar Juma’a, an saki ‘yan Koriya guda biyu da aka yi garkuwa da su. Dukkansu suna cikin koshin lafiya, kuma an kai su wani wuri mai tsaro inda suka yi magana da iyalansu bayan an duba lafiyarsu a asibiti,” in ji sanarwar.

Sanarwar ba ta yi bayani kan ko sai da aka biya kuɗin fansa kafin a saki mutanen ba.

Sai dai Ma’aikatar Harkokin Wajen ta Koriya ta Kudu ta ce an sake su ne sakamakon “haɗin gwiwa” da aka yi tsakanin gwamnatin Seoul da kamfaninsu da sojoji da ‘yan sanda da kuma jami’an leken asirin Najeriya.

Ta ce Koriya ta Kudu za ta sake nazari game da tsaron lafiyar ‘yan kasarta da ke aiki a Najeriya.

Yankin Neja Delta mai arzikin man fetur ya yi kaurin suna wajen sace-sacen jama’a musamman ‘yan ƙasashen waje a shekarun baya. Sai dai a baya bayan nan lamarin ya lafa.

Leave a Reply