An sake samun katsewar layin wutar lantarki a Najeriya

0
176
An sake samun katsewar layin wutar lantarki a Najeriya

An sake samun katsewar layin wutar lantarki a Najeriya

Daga Jameel Lawan Yakasai

Wutar lantarki a Najeriya ta sake katsewa a wannan ranar ta Laraba, rahoton Hukumar Independent System Operator (ISO) ya nuna cewa ƙarfin da ake samarwa ya sauka daga megawatts 2,917.83 zuwa megawatts 1.5 kacal tsakanin ƙarfe 11 na safe zuwa 12 na rana, matsalar da ta jefa sassa da dama na ƙasar cikin duhu.

Kamfanin rarraba wutar lantarki da ke babban birnini Tarayya Abuja (AEDC) ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar ga kwastomominsa,

Inda ya bayyana cewa katsewar ya faru ne da misalin ƙarfe 11:23 na safe sakamakon katsewar wutar daga babbar tashar lantarki ta kasa.

AEDC ta ce wannan ne ya haddasa rashin wuta a yankunan da ke ƙarƙashin ikon kamfanin.

KU KUMA KARANTA: Akwai barazanar katsewar wutar lantarki a faɗin Najeriya

A cewar AEDC, ana aiki tare da hukumomin da abin ya shafa domin dawo da wutar lantarki da zarar an daidaita tsarin.

Kamfanin ya kuma roƙi al’umma da su kwantar da hankalinsu tare da nuna haƙuri da fahimta, yana mai tabbatar da cewa za a dawo da wutar da wuri idan an kammala gyara.

Leave a Reply