No menu items!

Sample Page Title

Date:

An sake naɗa Okonjo-Iweala a matsayin shugabar WTO

Okonjo-Iweala ita ce mace kuma ‘yar Afirka ta farko da ta fara riƙe wannan muƙami tunda aka kafa ƙungiyar.

An Sake nada Dakta Ngozi Okonjo-Iweala a matsayin shugabar Kungiyar Cinikayya ta Duniya WTO a wani sabon wa’adin shekaru hudu.

Wa’adin zai fara ne daga ranar 1 ga watan Satumbar 2025 kamar yadda shafin shafin yanar gizon WTO ya wallafa a ranar Juma’a.

“Matakin ya nuna cikakken amincewa da jagorancin ta na musamman da hangen nesan ta na ci gaban WTO nan gaba.” A cewar shafin na WTO.

KU KUMA KARANTA:‘Yansandan Najeriya sun kashe mutane 24 a zanga-zangar tsadar rayuwa a watan Agusta – Amnesty

An fara aikin sake nadin nata tun a ranar 8 ga Oktoba, 2024, wanda Jakada Petter Ølberg daga kasar Norway, wanda shi ne Shugaban Majalisar Dinkin Duniya, ya jagoranta.

“Tunda babu wani karin dan takara da aka gabatar kafin wa’adin ranar 8 ga Nuwamba ya cika, Dr. Okonjo-Iweala ita ce kaɗai ta tsaya takara.” A cewa Majalisar Kolin kungiyar ta WTO.
An gudanar da wannan mataki cikin tsari da gaskiya, daidai da dokokin WTO kan “Tsare-tsaren Nadin Daraktoci Janar mai lamba (WT/L/509).”

Dr. Okonjo-Iweala wacce ‘yar asalin Najeriya ce, ta fara wa’adinta na farko a ranar 1 ga watan Maris 2021. Ita ce mace ta farko kuma ‘yar Afirka ta farko da ta fara rike wannan mukami

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...