An sace biliyan 50 daga asusun gwamnatin Kano – Muhyi Magaji

0
101
An sace biliyan 50 daga asusun gwamnatin Kano - Muhyi Magaji

An sace biliyan 50 daga asusun gwamnatin Kano – Muhyi Magaji

Daga Ali Sanni

Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta jihar Kano, ta bankaɗo badaƙalar satar kuɗi sama da naira biliyan hamsin a ƙananan hukumomi guda 44 dake jihar.

Shugaban hukumar, Muhyi Magaji Rimin Gado ya ce hukumar ta kuma gano wata badaƙalar naira miliyan 450 da aka sace daga asusun jihar da sunan sayen gidajen sauro masu ɗauke da magani.

Ya shaida wa mahalarta wani taron ƙara wa juna sani cewar, “mun gano naira biliyan 50 da aka sace daga asusun jihar, kuma ina da shaidu kimanin 145.

“Sannan mun gano wasu gidaje da otel-otel masu alaƙa da kuɗaɗen sata a biranen Dubai, London, da kuma Abuja.”

KU KUMA KARANTA: Gwamnatin Kano ta maka Ganduje da Garo a kotu bisa zargin karkatar da Naira biliyan 57

A cewarsa, da hukumar ta yi yunƙurin binciken wanda ake zargi da baɗakalar naira miliyan 450 na gidajen sauro, amma ya garzaya kotu neman umarnin hana ta binciken shi.

Muhyi ya bayyana wa mahalarta taron, waɗanda jami’an hukumomin yaƙi da rashawa ne daga jihar da ma tarayya cewa, kashi 80% na satar kuɗin gwamanti da aka yi a jihar Kano, an yi ne da sunan sayen kayan gwamnati.

Ya ce hanyoyin sun haɗa da aringizon farashi, sayen ƙasa da abin da aka tsara, ko ma rashin yin sayayyar bayan an biya kuɗaɗen.

Da yake jawabi, wakilin daraktan hukumar EFCC Shiyyar Kano a taron, CSP Aminu Bashir, ya bayyana cewa kashi 95% na satar kuɗaɗen gwamnati ana yin sune a wurin yin sayayya.

Don haka ya shawarci jami’an gwamnati da su riƙa bin ƙa’idoji da dokokin yin sayayyar gwamnati domin guje wa fushin shari’a ko shiga rikici.

A nasa ɓangaren, gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, wanda mataimakinsa, Aminu Abdulsalam Gwarzo, ya wakilta ya bayyana cewa, satar kuɗaɗen gwamnati ba ta yiwuwa sai da haɗin bakin jami’an gwamnati.

Ya ce gwamnatin Abba ba za ta lamunci satar kuɗin gwamanti ko rashawa ba, domin a cewarsa, jihar Kano ta ga mummunar illar satar kuɗin gwamanti a shekaru takwas da suka gabata, wanda hakan ya hana jihar samun ci gaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here