No menu items!

Sample Page Title

Date:

Daga Ibraheem El-Tafseer

Shugabar ƙaramar hukumar Fika a jihar Yobe, Hajiya Halima Kyari Joɗa ta jagoranci rushe gidajen karuwai haɗe da gidajen rawa na gala a garin Ngalda da ke ƙaramar hukumar Fika a jihar Yobe.

Kyari ita ce ta jagoranci rusa ɗakuna 140 a cikin gidaje 39, waɗanda suka haɗa da gidan karuwai da gidan sayar da giya a garin na Ngalda.

An ɗauki wannan ƙwaƙƙwaran mataki ne domin korar baɗala da ɓata tarbiyyar matasa maza da mata.

KU KUMA KARANTA: Gwamnan Gombe ya ba da umarnin rufe dukkan gidajen ‘Gala’ da ke jihar

Al’ummar garin Ngalda suna ta murna da wannan mataki, inda suke godiya ga Hajiya Kyari Joɗa. Sannan suna kira ga gwamnatin jihar Yobe da ta gaggauta gine waɗannan wurare da abubuwan da za su kawo ci gaba a garin na Ngalda da ma jihar Yobe ba ki ɗaya.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...