No menu items!

Sample Page Title

Date:

Hukumomin mulkin soja a Nijar sun rusa majalisun ƙananan hukumomi 266 da ke faɗin ƙasar da kuma shugabannin majalisun jihohi takwas waɗanda tuni aka maye gurbin su da wasu wakilai na musamman wato administrateurs délégué.

An bayyana haka ne a wata sanarwa da aka karanto a gidan talbijin na ƙasar ranar Alhamis da daddare.

“An rusa majalisun ƙananan hukumomi da kansiloli da wakilan larduna,” in ji sanarwar ba tare da bayyana dalilin ɗaukar matakin ba.

An maye gurabensu da jami’an soji da na ƴan sanda da wasu ma’aikatan gwamnati.

Shugaban mulkin sojin ƙasar Janar Abdourahamane Tiani ne ya sanya hannu a kan dokar da ta rusa majalisun ƙananan hukumomin da na larduna, in ji gidan talbijin na Tele Sahel.

KU KUMA KARANTA: Shugaban mulkin sojan Nijar ya tattauna da Putin kan haɗin gwiwar tsaro

Shugabannin da aka rusa zaɓaɓɓu ne kuma kundin tsarin mulkin Nijar ya ba su wa’adin shekaru bakwai na jagorancin ƙananan hukumomin.

Kazalika an sauke magajin birnin Yamai, Oumarou Dogari, daga kan muƙaminsa inda aka maye gurbinsa da wani kanar na soji.

A makon jiya ma’aikatar Ministan Cikin Gida da Ayyukan Ƙananan Hukumomin ke ƙarƙashin kulawarta ta haramta wa shugabannin ƙananan hukumomin kashe kuɗaɗe sai dai abin da ya shafi biyan albashin ma’aikata.

A watan Yulin da ya gabata ne sojoji suka yi wa gwamnatin farar-hula ta Mohamed Bazoum juyin mulki lamarin da ya sanya ƙungiyar ECOWAS ta dakatar da ƙasar daga cikinta.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...