An rufe makarantar da ɗalibai suka ci zalin wata yarinya a Abuja (Bidiyo)

0
222

Hukumomin wata makarantar sakandare mai zaman kanta a Abuja babban birnin Najeriya, Lead British International School sun sanar da rufe ta har na tsawon kwana uku, sakamakon rikicin da ya tayar da ƙura na “cin zalin wata yarinya da wasu ɗalibai suka yi.”

Wannan na zuwa ne bayan da wani bidiyo da aka nuna ɗaliban na cin zalin yarinyar, wadda ita ma ɗaliba ce ta hanyar dukanta ya karaɗe shafukan sada zumunta, tare da jawo Allah-wadai da kiraye-kirayen neman hukumar makarantar ta ɗauki mataki.

A sanarwar da hukumomin makarantar suka yi a wani bidiyo da aka yaɗa a shafukan masu faɗa a ji na Instagram a tanar Talata, an ga wani jami’in makarantar yana cewa an rufe ta bisa buƙatar da Ma’aikatar Mata ta Najeriya ta nema na yin hakan.

“Bisa buƙatar Ministar Mata ta Najeriya, kuma da yake mu ƴan Najeriya ne da muke girmama doka da oda kuma a ƙarƙashin doka muke aiki. Saboda makarantarmu fitacciya ce kuma an yi mata rajista ƙarƙashin hukumar babban birnin Najeriya Abuja, a don haka, daga yau an rufe Lead British International School, Abuja, tsawon kwana uku,” in ji mutumin.

Tun da fari dai a ranar Litinin ne masu amfani da kafofin sada zumunta a Najeriya suka ringa yaɗa wani bidiyo da aka ga ɗaliban makarantar ta Lead British suna cin zalin wata ɗaliba ta hanyar dukanta.

A bidiyon, an ga ɗalibar sanye da kayan makaranta, yayin da wasu ɗaliban mata biyu suka tsaya a kanta suna kwaɗa mata mari, sannan wani ɗalibi namiji yana zaune a gefe yana dariya, sai kuma wasu ɗaliban da ake jiyowa suna zuga masu marin, yayin da ita wadda ake marin ta gaza yin kataɓus.

A ɗaya bidiyon kuma an gan su a wata baranda ta saman makarantar da alama sun tare yarinyar suna dukanta.

Shafuka da dama musamman a Instagram sun yi ta saka bidiyoyin tare da yin ƙira ga hukumomi da su shiga maganar, inda dubban mutane suka yi ta tsokaci suna bayyana ra’ayoyinsu, waɗanda mafi yawa caccakar yaran da aka ga sun aikata laifin ake yi.

Dama tuni makarantar ta ce ta kafa kwamiti da zai binciki tare da ɗaukar mataki kan zargin cin zarafin dalibar da takwarorinta dalibai suka yi.

A cikin wata sanarwa da makarantar ta wallafa a shafinta na Facebook ranar Talata ta ce ta damu da abinda ya faru, sannan tana daukar batun da matukar muhimmanci.

A sanarwar da Lead British International School ta fitar ta ce ta kwafa kwamitin da zai bincika batun, kuma tuni ya fara aiki tare da tattara bayanai da kallon bidiyon cin zarafin.

KU KUMA KARANTA: Ana ci gaba da gudanar da laifukan cin zarafin ɗan’adam a Habasha – Majalisar Ɗinkin Duniya

Ta ƙara da cewa za a taimaka wa yarinyar da aka ci zarafin nata tare da iyayenta ta hanyar ba su shawarwari da kuma duk wani tallafi da ya kamata.

Sannan makarantar ta ce su kuma daliban da suka ci zarafin takwarar tasu, “za mu yi aiki tare da su da iyayensu, za a ba su shawarwari da kuma ladabtar da su don hana faruwar irin hakan a gaba.”

Ba wannan ne karo na farko da aka fara samun zargin cin zalin ɗalibai ba a makarantu a Najeriya, an kai matakin da ake ganin abin ya zama ruwan dare, inda a wasu lokutan yakan fito daga malamai a kan ɗalibai ko kuma ɗalibai su ci zalin ɗalibai ƴan’uwansu.

Na bayan nan da ya faru har ya tada ƙura a ƙasar shi ne na watan Disamban 2021 inda wani ɗalibi a makarantar Dowen College Lagos, mai shekara 12, Sylvester Oromoni ya rasa ransa sakamakon zargin cin zalinsa da wasu ɗalibai suka yi.

Rahotanni sun ce ɗaliban sun yi wa Oromoni duka ne wanda daga baya ya yi ajalinsa. Sai dai hukumar makarantar ta ƙaryata zargin a lokacin.

Leave a Reply