No menu items!

Sample Page Title

Date:

An rufe jami’ar Kogi saboda zanga-zangar ɗalibai

Hukumomin Jami’ar Tarayya da ke Lokoja a Jihar Kogi, sun rufe jami’ar har zuwa wani lokaci domin daƙile ci gaba da asarar rayuka da dukiya.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun magatakarda kuma sakatariyar majalisar Jami’ar, Dokta Rebecca Aimiohu Okojie, a ranar Alhamis kuma ta bayyanawa manema labarai a Lokoja.

Hukumar Jami’ar ta yi zargin cewa, ɗaliban sun tare babbar ƙofar shiga jami’ar ne tun bayan haɗarin da ya yi sanadin mutuwar ɗaliban jami’ar biyar a ranar Litinin, wanda ya sa shiga harabar jami’ar ke da wuya.

KU KUMA KARANTA:Ɗaliban jami’ar Ibadan sun yi zanga-zanga kan rashin wutar lantarki na tsawon kwanaki 100

“Rufewar jami’ar ya biyo bayan asarar rayuka da ɗalibai biyar suka yi a wani mummunan haɗarin tirela a Felele, ranar Litinin 17 ga Fabrairu, 2025

“Tun faruwar lamarin, ɗalibai sun tare ƙofar jami’ar duk da kakkausar murya daga gwamnatin jihar da kuma ƙoƙarin da hukumomin jami’ar suka yi na a kwantar da hankula.

“Saboda haka, bisa shawarar hukumomin tsaro na jihar da kuma daƙile ci gaba da asarar rayuka da dukiya, shugaban jami’ar bayan shawarwarin hukumar ta yanke, shawarar a madadin majalisar jami’ar cewa jami’ar, jami’ar da rassanta za a rufe su har sai baba-ta-gani. Ɗalibai za su bar wuraren karatu kafin ƙarfe 12 na rana ranar Alhamis, 20 ga Fabrairu.”

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...