An rantsar da sabbin shugabannin ƙananan hukumomi a Adamawa

0
82
An rantsar da sabbin shugabannin ƙananan hukumomi a Adamawa

An rantsar da sabbin shugabannin ƙananan hukumomi a Adamawa

Daga Idris Umar, Zariya

Alkalin alkalan jihan Adamawa, Mai shari’a Hafsat Abdulrahman, ta rantsar da sabbin shugabannin ƙananan hukumomin jihar 21, ranar litinin cikin nasara

Lamarin ya biyo bayan zaɓen da hukumar zaɓe ta jihar (ADSIEC) ta gudanar a ranar Asabar 13 ga watan Yuli, inda jam’iyyar PDP ta lashe dukkan kujerun shugabannin 21 da na kansiloli 225 yayin da jam’iyyar NNPP, ta samu kujerar kansila daya a karamar hukumar Demsa.

Da yake jawabi a taron gwamna Ahmadu Umaru Fintiri, ya kalubalanci shugabannin da su guji hanci da cin rashawa tare da rungumar kowa da kowa a gwamnatinsu.

Gwamnan ya kuma gargaɗi sabbin shugabannin da kansiloli da su guji rashin zuwa aiki akan lokaci, domin gwamnati mai ci ba za ta lamunci irin wannan dabi’a ta yadda shugaba zai yi watsi da aikinsa ba tare da wani dalili ba.

KU KUMA KARANTA: Tinubu ya yaba da hukunci kotun ƙoli kan ƙananan hukumomi

Gwamna Umaru Fintiri ya jinjinawa hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar ADSIEC bisa gudanar da zaɓen da aka amince da shi a matsayin wanda ya fi kowanne inganci a tarihin jihar Adamawa.

Haka kuma gwamnan ya taya shuwagabannin jam’iyyar PDP da shugabannin murnar nasarar da suka samu a lokacin zaɓen, ya buƙaci jama’a da su ci gaba da kasancewa masu biyayya da goyon baya ga gwamnatinsa domin ci gaban al’ummar jihar.

Shugaban jam’iyyar PDP na jihar Barista A T Shehu a jawabinsa, ya tunatar da shugabannin da aka rantsar cewa an zabe su ne bisa mutuncin gwamna Umaru Fintiri, inda ya buƙace su da su yi koyi da shi tare da samar da shugabanci na gari.

A jawabin godiya a madadin takwarorinsa, Suleiman Ahmed, sabon shugaban karamar hukumar Toungo, ya ce wa’adin da suke dashi na shekara biyu, ba zai wadatar ba muddin ba tare da kyakkyawan shugabancin gwamna Fintiri ya shimfida ba.

Ya kuma jaddada aniyarsu na gudanar da ayyukansu da kuma aiki bisa tsarin ci gaban wannan gwamnati mai ci domin amfanin al’ummar jihar Adamawa da ƙasa baki ɗaya.

Leave a Reply