An rantsar da mambobin hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa a Nijar

0
154

Shugaban Mulkin sojin Nijar Janar Abdourahamane Tiani wanda ya ɗare karagar mulkin ƙasar bayan kifar da gwamnatin Mohamed Bazoum a watan Yuli, ya rantsar da shugabannin hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa da kuma kotun jiha na ƙasar a hukumance a ranar Alhamis.

Kafar talabijin na ƙasar ce ta watsa taron bikin rantsawar guda biyu kai tsaye.

Sabbin shugabannin hukumar da na kotun sun yi rantsuwar fara aiki a gaban shugaban mulkin sojin ƙasar wato Janar Abdourahamane Tiani.

Taron na zama karo na farko da shugaban ya taɓa bayyana a bainar jama’a tun bayan da ya jagoranci hamɓarar da zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Mohamed Bazoum a ranar 26 ga watan Yuli.

Manyan hafsoshin soji da mambobin gwamnati da sarakunan gargajiya da malaman addini da kuma jami’an diflomasiyyar ƙasashen waje ne suka halarci bikin rantsarwar a babban birnin ƙasar, Yamai.

KU KUMA KARANTA: Lauyoyin Bazoum sun nemi kotu ta bayar da umarnin mayar da shi kan mulki a Nijar

Sabuwar kotun jihar za ta maye gurbin kotun sauraron ƙararrakin zaɓe da kuma ta majalisar dokokin jiha da aka rusa bayan juyin mulkin ƙasar.

A yanzu haka dai gwamnatin mulkin sojin ta buƙaci ta miƙa mulki ga farar hula nan da shekaru uku masu zuwa, sai dai ba a kayyade ranar da za a gudanar da zaɓe ba.

Babban aikin hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa shi ne ƙwato dukiyoyin al’umma da aka ƙwace ba bisa ƙa’ida ba.

Ma’aikatan hukumar sun ƙunshi alkalai da sojoji da jami’an ‘yan sanda da kuma wakilan al’umma.

Tiani ya yi alkawarin gudanar da taron tattaunawa na ƙasa, wanda zai taimaka wajen sanin ainihin lokacin da za a kwashe da kuma wa’adin mika mulki za su kasance.

Bazoum dai yana tsare a gidansa da ke tsakiyar fadar shugaban ƙasa tun bayan hamɓarar da shi.

Tun bayan juyin mulkin da ƙungiyar ECOWAS ta ƙaƙaɓawa Nijar takunkumin karya tattalin arziki, abin da ya janyo hauhawar farashin kayayyaki da kuma haifar da ƙarancin wasu kayayyakin da suka haɗa da magunguna.

Leave a Reply