No menu items!

Sample Page Title

Date:

An naɗa sabon darakta a kwalejin kiwon lafiya ta Al-Haroon Zariya

Majalisar Amintattu ta Kwalejin Kiwon Lafiya ta ‘Al-Haroon College Of Health Science and Technology’ da ke Zariya a jihar Kaduna ta naɗa Sani Musa Daitu, matsayin daraktan sadarwa na Kwalejin.

Kafin muƙamin sakataren yaɗa labaran kwalejin, Daitu Shine sakataren tsare – tsare na ƙungiyar matasan ‘yan Jaridu ta Jihar Kaduna (Kaduna Young Journalists Association KAYOJA).

Mustapha Aliyu Galadimawa shi ne Shugaban Majalisar Amintattun,  ya sanya hannu  amincewa da naɗin.

Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafukan Sada Zumunta, Musa Daitu ya ce “ina farin cikin sanar da ku cewa, ni, Sani Musa Daitu, an naɗa Ni a matsayin Daraktan Sadarwa a Kwalejin Kiwon Lafiya ta Al-Haroon da ke Zaria.”

Ya ce, an ba shi muƙamin ne wanda zai riƙe na tsawon shekaru uku (2024-2027), ya na mai alƙawarin zai yi aiki tuƙuru wajen ganin an cimma manufofin ofishin da ma na kwalejin.

KU KUMA KARANTA: Gwamnan Bauchi ya naɗa Alhaji Haruna Ɗanyaya a matsayin sabon Sarkin Ningi

Ya ƙara da cewa, zai bada gudunmawa da ƙwarewarsa wajen samar da nasarori da ci gaba musamman kan salon yaɗa labarai da sadarwa na kwalejin.

Har’ilayau, ya miƙa godiyarsa ga Majalisar amintattu ta kwalejin kan damar da suka ba shi ta aiki wajen samar da cigaba a ɓangaren harkar ilimi a Najeriya.

Sani Musa Daitu, Tsohon Wakilin Jaridar Amana Newspaper Abuja a Kaduna inda  ya riƙe muƙamin Mataimakin Shugaban Sashen Watsa Labarai da Al’amuran yau da kullum na Jaridar.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...