Connect with us

Ƙasashen Waje

An naɗa tsohon shugaban ‘yan daba Ministan Wasanni na Afirka ta Kudu

Published

on

An naɗa tsohon shugaban 'yan daba Ministan Wasanni na Afirka ta Kudu

An naɗa tsohon shugaban ‘yan daba Ministan Wasanni na Afirka ta Kudu

A wannan makon ne aka naɗa tsohon shugaban ƙungiyar ‘yan daba mai shekaru 50 a cikin majalisar ministocin ƙasar Afirka ta Kudu yayin da ƙasar ta kafa gwamnatin haɗin kan ƙasa (GNU) da Shugaba Cyril Ramaphosa ya ƙaddamar.

Hakan dai na zuwa ne bayan da jam’iyyar ANC mai rinjaye ta rasa rinjayen ‘yan majalisar dokokin ƙasar inda aka tilasta mata shiga ƙawance da jam’iyyun adawa.

An naɗa McKenzie – shugaban jam’iyyar Patriotic Alliance (PA) a matsayin Ministan Wasanni, Fasaha da Al’adu.

Kuma a ranar Laraba aka rantsar da shi tare da sauran takwarorinsa na majalisar ministocin, kuma ko a wajen sai da ya sanya mutane raha cikin barkwanci wanda ke nuni da irin laifin da ya aikata a baya.

“Lokaci na ƙarshe da wani alkali ya buƙaci na zauna, sai zaman ya zo da yanke min hukunci na tsawon shekara 10 a gidan yari,” ya faɗa cikin raha a lokacin da alkalin alkalan ƙasar Raymond Zondo ya buƙaci ya zauna don ya sanya hannu kan takardar rantsuwar zama minista.

“Wannan ya daɗe da wucewa)!” Alkalin Alkalan ya amsa da dariya tare da waɗanda suka halarci taron.

KU KUMA KARANTA: Yalon kati ya hana Slovenia hawa mataki na biyu a guruf ɗin gasar Euro 2024

Magoya bayan McKenzie sun ce labarin rayuwarsa daga zama shugaban ƙungiyar ‘yan daba a lokacin da yake da shekaru 16 zuwa zama minista a gwamnati, lamarin da ba a taɓa yin irinsa ba, wani ƙwarin gwiwa ne na shawo kan matsalolin rayuwa.

“Rayuwata ta ƙunshi shiga da fita gidan yari. Ba da daɗewa ba na zama wanda ake nema ruwa a jallo a sassa daban-daban na ’yan sanda. An kama ni ina da shekaru 21 a ƙarshe, ”in ji Ministan a cikin wasu jerin saƙonni da ya wallafa a shafin X.

“Na bayyana a kotu kuma an yanke min hukuncin ɗaurin shekaru 17 a gidan yarin Grootvlei.”

A lokacin, zuwa gidan yari tamkar alama ce ta girmamawa, in ji McKenzie. “Ba da daɗewa ba na yi shugabancin fursunonin gidan yarin gaba ɗaya kuma babu abin da zai faru a gidan yarin ba tare da na faɗa ba.”

Bayan an sake shi ya tsunduma cikin harkokin kasuwanci daban-daban – tun daga sayar da kifi, da gudanar da gidajen rawa da kuma saka hannun jari a harkar hakar ma’adinai.

Ya kuma kafa kamfanin buga littattafai da sayar da litattafai masu motsa rai daga abubuwan da suka faru a rayuwarsa.

Ya zama miloniya ta ƙiyasinsa. Amma sai da ya yi hatsarin mota kafin ya kai ga fara ganin sauyin rayuwa.

Ba da jimawa ba ya mayar da hankalinsa kan harkokin siyasa inda ya kafa jam’iyyarsa ta Patriotic Alliance a shekarar 2013 wacce ke da matsananciyar matsaya a kan harkokin shige da fice.

Ta lashe kashi biyu cikin 100 na ƙuri’un da aka kaɗa a ƙasar a zaɓen na ranar 29 ga watan Mayu, tare da nuna ƙwazo a lardin Western Cape, inda ta samu kashi takwas cikin 100 na kuri’un. Ta lashe kujeru tara na Majalisar Dokoki ta Kasa.

Lokacin da Shugaba Ramaphosa ya fara zawarcin jam’iyyun da za a kafa gwamnatin hadin gwiwa, McKenzie ya fito fili ya bayyana sha’awarsa ga ma’aikatar harkokin cikin gida, mai kula da shige da fice. Sai dai ya ƙara da cewa zai kasance mai gaskiya a tattaunawar.

“Ba mu da isassun kujerun da za su sanya mu a matsayin da za mu shata layi,” in ji shi a cikin wani sakon X.

“Za mu saurari shawarar shugaban ƙasa kuma za mu mutunta ‘yancin da kundin tsarin mulki ya ba shi na yanke shawarar wanda yake so a majalisarsa.”

Majalisar ministocin Ramaphosa mai mambobi 32 tana da ƙarin mataimakan ministoci 43 kuma ta sha suka daga jama’a da cewaan debi mutane da yawa a lokacin da ake cikin halin taɓarɓarewar tattalin arziki. Duk da haka, McKenzie yana da kyakkyawan fata game da sakamakon gwamnatin haɗin gwiwar.

“Rayuwa ta koya mani cewa wani lokacin yana da kyau a yi fada daga ciki fiye da daga waje, hakan kuma ya koya min cewa a cikin tattaunawar ba za ku taba samun duk abin da kuke so ba.
Ina son Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida, ban samu ba,” kamar yadda ya wallafa a shafin X bayan sanar da jerin sunayen ministocin.

McKenzie ya yi alkawarin bayar da dukkanin albashinsa na majalisa ga gidauniyar Joshlin Smith da ke kula da yaran da suka ɓace, kamar yadda kafafen yaɗa labarai na cikin gida suka ruwaito.

“Kashi 100 na albashina zan bai wa gidauniyar Joshlin Smith mai kula da harkokin yaran da suka ɓace na tsawon zamana a majalisar, kashi 100 na albashina ba 80% ko 50% ba… Saboda ban zo nan don kuɗi ba. Na zo ne domin in sauya rayuwar mutanenmu,” in ji shi.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Ƙasashen Waje

Isra’ila ta kama mutum 15 a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan

Published

on

Isra'ila ta kama mutum 15 a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan

Isra’ila ta kama mutum 15 a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan

Aƙalla Falasɗinawa 15 Isra’ila ta ƙara kama a wani samame da ta kai a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan da ta mamaye, kamar yadda wata ƙungiya da ke kula da fursunoni ta tabbatar a ranar Lahadi.

Sojojin sun kai samamen ne a Hebron da Tubas da Ramallah da Birnin Kudus, kamar yadda hukumar da ke kula da waɗandake tsare da kuma ƙungiyar kula da fursunoni Falasɗinawa suka bayyana a wata sanarwa ta haɗin gwiwa.

KU KUMA KARANTA: Hezbollah ta harba rokoki 200 da jirage marasa matuƙa cikin Isra’ila

“Waɗanda aka kama na fuskantar cin zarafi da duka, da kuma barazana ga iyalansu, baya ga yawaitar ayyukan zagon kasa da lalata gidajen ‘yan ƙasar,” kamar yadda sanarwar ta ƙara da cewa.

Kamen na ranar Lahadi ya kawo adadin Falasɗinawa da Isra’ila ta kama tun daga 7 ga watan Oktoba a Yammacin Kogin Jordan zuwa 9,550 a cewar alkaluman Falasɗinawa.

Continue Reading

Ƙasashen Waje

Dakta Mas’ud Pezeshkian ne lashe zaɓen shugaban ƙasar Iran

Published

on

Dakta Mas'ud Pezeshkian ne lashe zaɓen shugaban ƙasar Iran

Dakta Mas’ud Pezeshkian ne lashe zaɓen shugaban ƙasar Iran

Daga Ibraheem El-Tafseer

Waye Dakta Mas’ud Pezeshkian sabon shugaban ƙasar Iran na 9 cikin shekaru 45 ataƙaice?

An haife shi a ranar 29 ga Satumba, 1954, a Mahabad, a yammacin lardin Azarbaijan, Dakta Mas’ud Pezeshkian ya wakilci birnin Tabriz da ke arewa maso yammacin kasar a majalisar dokokin Iran ta 12.

Ya riƙe muhimmin muƙamai a majalisar a Hukumomi daban-daban matakin gwamnatin tarayya, kuma ya zama ministan lafiya a lokacin mulkin Shugaba Mohammad Khatami (2001-2005). Duk da cewa an tsige shi bayan wasu lokuta saboda gaza cimma wasu ayyuka da kawo sauyi.

An zaɓe Pezeshkian a majalissar 8th, 9th, 10th, and 11th. A tsakanin shekarar 2016 zuwa 2020, ya kuma rike mukamin mataimakin shugaban majalisar na farko. A baya dai ya tsaya takarar shugaban kasa a shekarar 2013 da 2021 amma ya kasa samun nasara a lokuta biyun.

KU KUMA KARANTA: An kammala zagayen farko na zaɓen shugaban ƙasa a Iran

Dr. Mas’ud Pezeshkian likitan zuciya ne kuma me koyarwa, ya yi aiki a matsayin shugabar Jami’ar Tabriz ta Kimiyyar kiwon lafiya, kuma a halin yanzu memba ne na ma’aikatan ilimi a wannan babbar jami’a a arewacin Iran.

Bayan da ya samu amincewa daga babbar hukumar da ke sa ido kan zabukan kasar na ya tsaya takara a zaben na ranar 28 ga watan Yuni a watan da ya gabata. Ya gabatar da tsare-tsarensa, inda ya jaddada muhimmancin damka ayyuka ga kwararru kuma masu ilimi a gwamnatinsa.

Haka nan kuma ya bayyana Javad Zarif, tsohon ministan harkokin wajen kasar Iran a matsayin zabinsa na shugabancin ma’aikatar harkokin wajen kasar, yayin da ya sha alwashin aiwatar da umarnin Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei.

Pezeshkian a hukumance ya shiga takarar neman kujerar shugaban kasar a ranar 1 ga watan Yuni, rana ta uku ta rajista, a ma’aikatar harkokin cikin gida da ke Tehran, tare da rakiyar gungun magoya bayanta.

A muhawarar zagaye na biyu na zaben shugaban kasa, Pezeshkian ya bayyana mahimmancin kiyayewa da cika alkawura a matsayin wani muhimmin al’amari na kiyaye kyawawan halaye.

Ya jaddada muhimmancin nuna girmamawa ga daidaikun mutane, tabbatar da jin muryoyinsu, da bayar da shawarwari kan ayyuka bisa ka’idojin adalci da adalci.

Tsohon ministan lafiya ya kuma jaddada muhimmiyar rawar da amana ke takawa wajen ciyar da al’umma gaba, tare da jaddada cewa gaskiya na da matukar muhimmanci wajen samar da amana a tsakanin al’umma.

Pezeshkian ya jaddada muhimmancin ba da fifiko kan dangantaka da kasashen dake makwabtaka da ita, da fadada huldar dake tsakanin kasashen duniya don bunkasa ci gaban kasar.

A lokuta da dama, ya nanata kudurinsa na mutunta tsarin dokokin Jamhuriyar Musulunci da kuma manufofin da Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamene ya bayyana.

Continue Reading

Ƙasashen Waje

Hezbollah ta harba rokoki 200 da jirage marasa matuƙa cikin Isra’ila

Published

on

Hezbollah ta harba rokoki 200 da jirage marasa matuƙa cikin Isra'ila

Hezbollah ta harba rokoki 200 da jirage marasa matuƙa cikin Isra’ila

Daga Ibraheem El-Tafseer

Ƙungiyar Hezbollah mai da ke Lebanon ta ƙaddamar da hare-haren rokoki fiye da 200 da jirage marasa matuƙa zuwa arewacin Isra’ila, a wani martani na kisan ɗaya daga cikin manyan kwamandojinta.

Rundunar sojin Isra’ila ta ce an kashe sojanta da dama a hare-haren, na Hezbollah.

Sojojin na Isra’ila sun kuma ce sun mayar da martani kan mayaƙan ƙungiyar da sansanoninta da ke kudancin Lebanon.

Kafofin yaɗa labaran Lebanon sun ce mutum guda ya mutu a wani harin jirgi maras matuƙi da Isra’ila ta kai garin Houla.

Hare-haren na baya-bayan nan, sun kasance mafiya muni cikin watanni tara tsakanin kan iyakokin ƙasashen biyu.

KU KUMA KARANTA: Gaza ya zama gidan marayu kuma maƙabartar yara mafi girma a duniya – Emine Erdogan

An kashe ɗaya daga cikin kwamandojin Hezbollaha wani hari ta sama da Isra’ila ta kai birnin Tyre na ƙasar Lebanon.

Mohammed Nimah Nasser, ya kasance ɗaya daga cikin manyan jagororin ƙungiyar, kafin kisan nasa.

Continue Reading

GOCOP ACCREDITED MEMBER

You May Like