Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya haɗa wasu iyaye da yaransu da aka sace.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da sakataren watsa labaru ga gwamnan, Sanusi Bature ya fitar.
Gwamna Abba Kabir ya nuna farin cikinsa lokacin da yake bai wa iyayen ƴaƴansu, inda ya kuma yaba wa rundunar ƴan sandan jihar ta Kano bisa namijin ƙoƙari da suka yi wajen kuɓutar da yaran.
An miƙa shida daga cikin yaran bakwai da aka ceto ga iyayensu waɗanda ƴan asalin jihar Bauchi bayan nasarar da ƴan sandan Kano suka yi wajen kama mutanen da suka sace su.
Gwamnan ya buƙaci iyayen yaran da su rika sa ido kan ƴaƴansu domin tabbatar da halin da suke ciki a kowane lokaci.
KU KUMA KARANTA: ‘Yan sandan Kano sun kama mutum tara bisa zargin su da sayar da yara
Ya kuma yi ƙira ga takwaransa na Bauchi, Bala Mohammed, da ya ɗauki sassauran mataki ga dukkan waɗanda aka kama da laifin satar yara.
A martaninsu, iyayen yaran sun nuna godiya ga gwamnan Kano da kwamishinan ƴan sandan jihar kan ceto ƴaƴan nasu.
A ranar Alhamis, rundunar ƴan sandan jihar Kano ta yi nasarar kama wani gungun mutanen da suka ƙware wajen satar yara da kuma safararsu zuwa waɗansu jihohi a kudancin Najeriya.
Ƴan sanda sun ce an cafke mutanen ne a tsakanin jihohin Kano da Bauchi da Anambra da Imo da kuma Legas